Wani abin fashewa a garin Galkogo a jihar Neja ya kashe mutane da dama.
An rahoto cewa abin fashewar ya fi shafan mambobin jami’an tsaro na hadin gwiwa ne a yankin yayin sintiri.
A cewar wasu ruwayoyi biyu, luguden wuta da jiragen yakin NAF ko nakiya da yan bindiga suka jefa ne ya janyo fashewar.
Wasu mutane da dama sun rasu sakamakon abin fashewa da ya tarwatse a garin Galkogo, Karamar hukumar Shiroro, Jihar Neja, The Punch ta rahoto.
Ruwayoyi biyu kan afkuwar lamarin sun yi ikirarin cewa luguden wuta daga jiragen yaki na Sojojin Saman Najeriya, NAF, ne ya janyo fashewar yayin da wani ruwayar ya ce nakiya ce da yan bindiga suka jefa wa mazauna garin.
Da ya ke magana kan harin, wani mazaunin garin, Tanko Erena, ya ce luguden wuta daga jiragen NAF ne ya fada kan jami’an tsaro na hadin gwiwa da ke sintiri a yankin.
Erena ya ce akwai yiwuwar wadanda ke tuka jirgin yakin na NAF ba su san mambobin JTF ne abin ya shafa ba.
Kalamansa; “Na yi imanin wadanda ke cikin jirgin sun yi zaton mambobin na JTF yan bindiga ne don babu wani hujjar da zai sa su sakin musu bam.
“Zan iya fada maka cewa an ciro gawarwaki da yawa daga wurin da abin ya faru amma na ga motocci biyu da suka kwaso gawarwaki daga wurin.”
Sahara Reporters ta kuma rahoto cewa wasu yan ta’adda ne suka jefa wa mazauna garin abu masu fashewa.
Yayin ambato wani wallafa da wani kwararre kan harkoki tsaro ya yi, rahoton ya yi ikirarin cewa mutanen garin sun aika da sakon neman dauki bayan faruwar abin.
Kwararren mai suna @secmxx a Twitter, kamar yadda jaridar ta ambato ya ce; “Mazauna garin Galadiman Rogo kusa da dam din Shiroro a jihar Neja sun ta aika sakon neman dauki kan fashewar abubuwa a yankin, wasu rahotonni da ba a tabbatar ba sun ce wasu sun mutu.
“A yanzu ba a san ko su wanene abin ya shafa ba.”
Kwamishinan tsaron cikin gida da ayyukan jin kai na Jihar Neja, Emmanuel Umar, ya ce bai samu ji ta bakin kakakin yan sandan jihar, DSP Wasi’u Abiodun ba da Kakakin NAF Air Commodore Wap Maigida kan afkuwar lamarin.
Yan Ta’adda Sun Sace Mahaifiyar Dan Majalisa, Sun Kashe Mutum 2 A Neja Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi awon gaba da Haj Salamatu Ahmadu, mahaifiyar dan majalisar jihar Neja, Alh Bello Ahmed Agwara.
Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, an sace dattijuwar ne a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu misalin karfe 9 na safe.