A kwanakin baya ne wani Malamin Ahlul Sunnah a jihar Bauchi, Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya yi furucin cewa‘…Ko taimakon Manzon Allah ma ba su bukata. Kafin nan ya jero sunayen wasu Shehunnan Darika inda ya nuna cewa ba a neman agajinsu a yayin neman taimako.
Bayan yin jawabin nan nasa ne wasu ke ganin rashin ladabi wajen shigo da Manzon Allah (SAW) cikin misalinsa wanda kai tsaye wasu suka nuna hakan da rashin kimanta Manzon Allah. A kan hakan, hukumar shari’a ta jihar Bauchi ta aike da wasikar gayyata ga Malam Idris domin ya bayyana a gaban malamai domin wanke kansa ko kare kansa.
Kwanaki kadan da aike masa da wasikar gayyata ne wasu gungun Malaman Ahlul Sunna suka hallara a jihar Bauchi domin mara masa baya da shiga a dama da su a yayin mukabalar.
Sai dai a cikin jawaban wasu malaman da suka fito daga sassa daban-daban na kasar nan sun yi zafafan jawabai a kan malaman darika da har ‘yan Darika suka yi zargin an fito da sunayen Malamansu balo-balo aka zaga. Matakin da ya kai ga har zuwa gaban kotu.
Daya daga cikin ‘ya’yan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Malam Naziru Dahiru Usman Bauchi, ya ce, daga yanzu ba za su sake zura ido su na kallon wasu malaman Ahlul Sunnah su na zagi musu waliyyar ko Shehunnai su yi shiru ba, don haka ya ce sun kai kara kotu domin neman hakkinsu na zagin manyan malamansu da aka yi.
“Saboda shehunanmu sun ba mu tarbiyya a kan cewa kada mu rika daukan doka a hannunmu.
Amma fa idan muka ga gwamnati ba ta shiga ta kama wannan yaron da ya zagi wadannan bayin Allah ba, tare da kaishi gaban hukuma aka hukunta shi ba; don hakan su zama izina ga duk wadanda suke da niyyar yin irin wannan zage-zagen, to tabbas za mu fara daukan doka a hannunmu.
“Amma a halin yanzu muna biyayya wa malamanmu domin sun ce muke bin dokar kasa.
Amma in ba haka ba, Maulana Sheikh yana da al’umma da yawa masoya wadanda suke shirye su mika ransu saboda ba shi kariya, saboda sun san kare martaba addinin musulunci ya ke yi kare darajar Manzon Allah (SAW) yake yi da Shehu Tijjani da Shehu Ibrahim.
“Wanda zai zo karara ya kama sunansa ya zaga ko ya kama sunan Shehun nan din nan ya zaga neman tada hankali yake yi.
Wallahi in kuka bari muka fara fitowa a kan wannan abun ba za a sake samun zaman lafiya ba.”
Don haka ya ce, sun je kotu su nemi hakkinsu kamar yadda dokar kasa ta tanadar, “A kamo wadannan yaran da suka yi wannan zagin a tabbatar an hukunta su. Mun tara dukkanin hujjoji.”
Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, tunin suka kammala tsare-tsaren da suka dace na yin shari’ar nan tare da lauyoyinsu kuma a shirye suke su nemi adalci a kowani mataki na shari’a.
Daga bisani dan Shehin ya yi gargadin cewa muddin aka yi sake aka ki musu adalci, kuma wani ko wasu gungu suka sake zagi musu Shehu Ibrahim Inyas ko Shehu Tijjaniya ko Shehu Dahiru Bauchi ko kuma ya taba wani abu na martabar Annabi Muhammadu (SAW) ko da meye ya fake sai sun dauki doka a hannunsu domin ba za su cigaba da zura ido ana zagan musu shehun nan ba.
“Don haka yanzu haka dai mun bai wa mutanenmu hakuri kada kowa ya dauki doka a hannunsa in mun je kotu muka ga an maida abun shiririta ba a kamasu a hukuntasu ba, aka ja layi aka hana kowa sake zagi ba, wallah idan muka fara daukan doka a hannu lamarin ba zai yi kyau ba. Ba fata muke a kai wannan matakin ba, so muke yi a yi adalci domin ba mu kira ga tashin hankali.”
“Abu kawai ya zama yayi don mutum yana son ya yi suna sai ya kama zagin shehunai don kawai yana son a sanshi sai ya kama cin zarafin Dariku sufaye ya rika zagin Sufaye. Ka je ka yi addininka mana waye ya ce maka ka zagi wasu ko ka ci mutuncinshi. An ce muku idan muka fara zanga-zanga lamarin zai yi sauki ne?” ya yi gargadi.
Da ya ke bayani kan gayyatar da suka yi wa Malam Idris, shugaban hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar Bauchi, Malam Mustapha Baba Ilaleh, ya ce sun daye zaman ne domin kara shirye-shirye.
Ya ke cewa: “Lallai mun shirya za a yi zama da Malam Idris Abdul’aziz dangane da wasu kalmomi da ya fada; to kalmar karshe da ya furta sai ya zama ya yi wa al’ummar musulmai zafi musamman wadanda suka kasance masoyan Manzon Allah (SAW). To wannan kalmar ya daga hankali sosai a ciki da wajen gari. Hakan ya sa aka kira zama na musamman da shi aka kuma tanadi malamai domin a zo a zauna a tattauna da shi a ankarar da shi munanan kalma da ya ambata ko dai a yarda da muninsu don babu maganar kariya a wannan kalmar domin kalmomi ne wadanda da wuya su dauki wani tawili.
Wannan ya sanya muka yi shirye-shirye domin a yi a ranar Asabar 8 ga watan Afrilu amma sakamakon wasu abubuwa da muka ga ya dace mu kammala su mu tanadasu ya sa muka ga ya dace mu daga daga baya za a yi wannan zaman.”
“Shi wannan zaman mun shirya shi ne sakamakon wata ibara wato wata jimla da shi Malam Idris ya fada lokacin da yake kokarin kore istigasa da istina neman taimako ko neman agaji ba a yi a wajen kowa sai Allah (SWT), ya ce, baya nema a wajen Inyasi, ba ya nemi a wajen Tijjani ba ya nema a wajen Abdulkadiri ba ya nema a wajen Shehu Danfodio sai ya ce kai ko (Wa’izabilla) ko Manzon Allah ma ba mu neman taimako a wajensa, ‘ko Manzon Allah ma ba mu bukatar taimakonsa’, wa’iyazubillah.
“To ka ga wannan wata jimlace da ba za ta dauki wani tawili ba. Malamai suke fassara wannan jimlar da cewa akwai ihana ga Annabi (SAW) wato akwai kaskantawa ga Annabi (SAW) kuma akwai abun da ake kira ‘su’ul’adabi’ wadannan suka sabbaba muka ga ya kamata a nemeshi ya zo ya yi bayani tattare da wannan jimlar tasa ta karshe don mu a kanta muke magana. Da kuma munanta ladabi wadanda bai kamata ya fadi wadannan kalmomin ba.”
Malam Mustapha Ilaleh ya karyata batun da ke cewa sun dage zaman ne sakamakon janyewa da kungiyar Izalah ta yi a wajen zaman, ya ce sam ba wannan ne dalilin da ya janyo dage zaman ba domin tun kafin kungiyar ta aiko da wasikarta sun riga ma sun cimma matsayar dage zaman.
Ya ce, makasudin shirya zaman shi ne domin a tabbatar da yin gaskiya da fito da batutuwa daga littafai na magabata.
Daga nan Baba Ilaleh ya yi kira ga al’umma da a kowani lokaci suke amsar tacaccen ilimi sannan jama’a su kara sanin hakkokin Manzon Allah (SAW) don a so shi so ta gaskiya ta hakika a bi shi bi ta sunnar gaske ba ta riyawa a baki ba kawai.
A cewarsa, akwai bukatar a kullum a ke amfani da hujja mai karfi da hujja mai asali tare da bin fassara da ma’anoni kamar yadda magabata suka bayar a sullisi na Kur’ani ko hadisai.
Daga nan ya jawo hankalin jama’a da cewa koda irin wannan abun ya faru kada su dauki doka a hannunsu kuma kada su furta kalamai marasa kan gado domin ya bada tabbacin cewa za su bi lamarin kuma za a fito da hakikanin abubuwan da suka dace.
Ita kuma Gwamnatin Bauchi ta gargadi malamai ne kan amfani da kalaman tunzura jama’a da nufin wanzan da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.
Sakataren gwamnatin jihar, Mista Ibrahim Kashim ne ya yi wannan gargadin yayin da yake zantawa da manema labarai sakamakon taron kwamitin tsaro na jihar, a ranar Litinin a Bauchi.
A cewarsa, gwamnati za ta tunkari duk wani mai wa’azi da ya yi kalaman da zai iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin jama’a.
“Kamar yadda kuka sani, muna fitowa ne daga cikin mawuyacin halin da ake ciki na yakin neman zabe kuma abubuwa da dama sun faru bayan zaben da ke bukatar tsauraran matakan tsaro.
“An yi ta hayaniya wasu kuma kan batutuwan da suka shafi wa’azi da fahimtar mahallin wa’azi da kuma abin da ya haifar.
“Mun damu saboda ba batun ‘Akida’ ba ne, ba batun siyasa ba ne kawai batun tunzura maganganun da za su haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummarmu.
“Mun gana, mun tattauna kuma mun yanke shawarar cewa Bauchi wuri ne mai matukar zaman lafiya, kuma za mu yi duk abin da za mu iya don ganin an zauna lafiya.
“Ba za mu bari wani abu ko maganganun wani ya kawo cikas ga zaman lafiyar da muke samu a jihar ba,” in ji shi.
Kashim ya kara da cewa gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, “Ba za mu kyale wani daga yanzu ya ci mutuncin wani ko cin mutuncin imanin wani ko wasu mutane dangane da imaninsu ba,” in ji shi.
Shi ma da yake jawabi, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aminu Alhassan, ya bayyana cewa ana kokarin dakile ayyukan da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.
Source:LeadershipHausa