Akalla fursunoni 240 ne suka tsere daga gidan yarin Kabba da ke jihar kogi a tarayyar Najeriya biyo bayan wani farmaki da tsakaddare da ba a kai ga gano wadanda ke da alhakin kaddamar da shi ba.
Tuni dai hukumar kula da gidajen yarin Najeriyar ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta Mr Francis Enobore inda cikin wata sanarwa ya bayyana cewa wani gungun ‘yan bindige rike da makamai ne suka afkawa gidan yarin da tsakaddare.
Kwanturolan hukumar Halilu Nababa ya bukaci daukar matakin dawo da wadanda suka tsere daga gidan yarin baya ga tsananta bincike don gano masu hannu a harin cikin gaggawa.
Haka zalika hukumar ta bukaci al’ummar jihar da makwabtanta su bayar da hadin kai wajen kai bayanan duk wasu da suke zargi ga mahukunta don mayar da fursunonin gidajen yarin.
A shekarar 2008 ne Gwamnati ta samar da gidan yarin na Kabba da ke daukar mutane 200 yayinda yanzu haka ya ke dauke da mutane 294 ciki har da 224 da ke jiran shari’a yayinda 70 ke matsayin ‘yan gidan yarin na hakika.
A wani labarin na daban Iran ta ce tana ci gaba da tattaunawa da Amurka kan musayar fursunoni, bayan da Washington ta tabbatar da cewa, ana kokarin karbo ‘yan kasar da aka tsare a wasu kasashen.
Malley ya tabbatar cewa hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin Amurka na tabbatar da karbo ‘yan kasar da ke tsare a wasu kasashen, yana mai cewa ana samun ci gaba a tattaunawar da Amurkan ke yi da kasar ta Iran.
Wadannan kalaman na zuwa ne yayin da Iran ta shiga tattaunawa da manyan kasashen duniya a Vienna kan farfado da yarjejeniyar nukiliyarta ta shekarar 2015.
Yarjejeniyar, wacce aka yi game da takaita shirin nukiliyar Iran don sassautawa kasar takunkumi da aka kakaba mata, ta kasance cikin halin mutu kwa-kwai rai kwa-kwai tun lokacin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar a shekarar 2018 inda ya sake sabunta takunkumin a wancan lokacin.
Tun daga lokacin ne kuma kasar ta Iran ta kara kaimin cafke mutanen da ake zargi da laifin leken asiri.
Kasashen biyu a cikin watan Mayu sun musanta cewa sun kammala yarjejeniyar musayar fursunoni, bayan rahotanni da ke cewa an yi yarjejeniya bayan tattaunawar ta Vienna game da sakin fursunoni hudu daga kowane bangare.
Da aka tambaye shi game da kalaman na Malley, kakakin gwamnatin Iran Ali Rabiei ya tabbatar da tattaunawar kuma ya ce gwamnati na kira da a saki dukkan fursunonin Iran din, ba wai iya wadanda suke tsare a Amurka ba kawai.