Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki garin Funtua da ke karamar hukumar Funtua a jihar Katsina, inda suka kashe akalla mutum daya a daren ranar Litinin.
Wanda lamarin ya rutsa da shi, kansila ne mai wakiltar mazabar Nasarawa ta karamar hukumar Funtua, Samaila Buhari Mairago, an ce an kai masa hari ne a gidansa da ke unguwar Nasarawa a cikin garin.
Ba a dai bayyana dalilin kashe shi ba, amma ana zargin samun rashin nasara ne wajen kokarin yin garkuwa da shi. Da yawan masu amfani da shafukan sada zumunta sun tabbatar da harin da kuma mutuwar kansilan.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, yankin na fama da hare-haren ‘yan bindiga akai-akai a ‘yan kwanakin nan.
A wani labarin na daban rundunar ‘yansandan jihar Taraba a ranar Litinin ta tabbatar da mutuwar wasu mutum hudu sakamakon wutar lantarki a yankin Danyavo da ke Jalingo, babban birnin jihar.
Bayanai sun yi nuni da cewa, an kawo wuta mai karfi ne a unguwar, lamarin da ya janyo bugawar taransifoma har ya janyo hakan.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abdullahi Usman, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Jalingo.
A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Litinin.
Jami’in ya bayyana cewa, wadanda lamarin ya rutsa da su, sun hada da Remond Ofonbuk, dan shekara 44 a duniya, da matarsa, Mfonbong Remond, Hevean Remong dan shekara 15, da kuma First Remond dan shekara 13.
Usman ya ce, an ajiye gawarwakin mamatan a dakin adana gawarwaki domin gano hakikanin abun da ya janyo tashin gobarar.
Source LEADERSHIPHAUSA