A wani sumame d suka gabatar, dakarun Operation Hadarin Daji da ke yankin Arewa maso Yamma suka yi, sun kubutar da daliban jami’ar Tarayya Gusau (FUGUS) ta jihar Zamfara hudu, wadanda wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su ranar Asabar.
Kamar yadda kafar yada labarai ta PRNigeria ta ruwaito, an sace daliban ne daga gidan da suke a unguwar Sabon Gida da ke yankin Damba a karamar hukumar Gusau, babban birnin jihar.
‘Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Jami’ar Tarayya Ta Gusau (FUGUS) Sun Sace Dalibai
Sojoji Sun Ceto Wasu Karin Dalibai Mata 7 Na Jami’ar Tarayya Da Ke Gusau Jihar Zamfara
Wata majiyar leken asiri ta tsaro ta bayyana cewa, dakarun Operation Hadarin Daji sun toshe duk wata babbar hanyar fita daga wajen don tunkarar ‘yan bindigar.
“Ba tare da bata lokaci ba sojojin suka tattara tare da kafa wani shinge a hanyoyin wanda ya kai ga yin artabu da ‘yan ta’addar.
“Karfin da sojoji ke da shi ya sa ‘yan ta’addar suka yi watsi da wadanda lamarin ya rutsa da su suka gudu.
A yayin arangamar da ‘yan ta’addar biyu daga cikin daliban suka tsere yayin da wasu jiga-jigan sojojin suka ceto sauran mata biyu da namiji da lamarin ya rutsa da su cikin koshin lafiya,” kamar yadda PRNigeria ta rawaito.
Kazalika, kakakin rundunar ‘Operation Hadarin Daji, Captain Yahaya Ibrahim, da aka tuntube shi, ya tabbatar da nasarar da aka samu na ceto daliban jami’ar.
Source LEADERSHIPHAUSA