Jami’ar Tarayya da ke Birnin Kebbi, FUBK ta gudanar da bikin daukar dalibai 2,217 da za su yi karatun digiri na farko da na biyu a Fanni daban-daban, a harabar jami’ar da ke Unguwar jaji a karamar hukumar Kalgo a Jihar.
An kafa jami’ar ne a cikin shekarar 2013 kuma ta fara karatu tare da dalibai a cikin shekarar 2014 inda take da sashin digiri 24, ya zuwa yanzu tana da sashin karatun digiri 37 da sashin karatun gaba da digiri na farko guda 20.
A nasa jawabin, Shugaban jami’ar Farfesa Zayyan Muhammad Umar ya bayyana cewa, jami’ar a shirye take ta yi amfani da kudadenta tare da karfafa ribar da take samu a halin yanzu domin bude sabbin hanyoyin samun dama ga ma’aikatanta da dalibanta.
Wannan bikin taron daukar Dalibai da jami’ar ta yi dai, shi ne karo na 9 tun bayan kaddamar da Jami’ar a shekarar 2013.
“Jami’ar FUBK ta karbi bukatar dalibai 2,530 da suka nemi gurabun karatun digiri na farko a jami’ar a wannan zango, an bai wa dalibai 2,269 damar yin rajista amma 2,095 ne kadai suka yi nasarar samun gurbin karatu.
DUBA NAN: Jam’iyyar APC Tazo Ne Domin Talakawan Adamawa
“A matakin digiri na biyu, an samu jimillar Dalibai 112 da suka nema, kuma duk suna ci gaba da karatunsu a halin yanzu.” inji shi.