Fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce ba zai taba barin El-Rufai shiga gidansa ba.
Fitaccen malamin ya sanar da hakan ne yayin da ya karba bakunci korarren Sarkin Kano, Sanusi Lamido a gidansa dake garin Bauchi
Malamin ya zargi El-Rufai da kwashe masa almajirai tare da muzgunawa mazauna gidansa saboda makaranta Qur’ani ne Fitaccen Malamin addinin Islama,
Sheikh Dahiru Usman Bauchi, yace babu dalilin da zai sa ya bar Gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai ya shiga gidansa idan da ya biyo tawagar tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi.
Idan za mu tuna jami’an jihar Kaduna dake tabbatar da yaki da bara sun shiga makarantar malamin inda suka kwashe almajirai a shekarar da ta gabata, Vanguard ta wallafa.
Sheikh Bauchi ya sanar da hakan ne a gidansa dake Bauchi a ranar Litinin yayin da ya karba bakuncin tsohon sarkin wanda aka nada Khalifan Tijjaniya a Najeriya.
“Ina El-Rufai? A zatona ai zai biyo tawagarka, da na sa masu gadi sun hana shi shigowa koda farfajiyar gidan nan.
Ya kori dalibai masu koyon karatun Qur’ani, ya zuba su a daji kuma ya dawo gidana ya hantari mutanen dake ciki saboda kawai makaranta Qur’ani ne,” Sheikh Dahiru yace.
A bangarensa, korarren sarkin kano Alhaji Lamido Sanusi ya roki yafiya a madadin abokinsa inda yace yana da tabbacin gwamnan bai san abinda ya faru ba.
“El-Rufai baya kasar lokacin da lamarin ya faru, nima bana Najeriya yayin da hakan ta faru.
Ina tabbatar maka da cewa hakan ba zai sake faruwa ba.
Ina rokon yafiya a madadin abokina kuma aminina. “Ina fatan lamarin bai shiga har zuciyarka ba saboda abun ba zai yi dadi ba idan hakan ta faru. Babu wanda zai yi fatan ya zama makiyi a idanun mutum irinka. Ka yafe mishi har cikin zuciya,”Sabon shugaban Tijjaniyan ya roka.
A wani labari na daban, kafin fara yajin aikin kwanaki biyar na jan kunne da kungiyar kwadago ta Najeriya ta shirya farawa a ranar Litinin a jihar Kaduna,
Gwamna Nasir El-Rufai yace ya shirya kuma yana jiran shugabannin kungiyar kwadagon da na jam’iyyar adawa ta PDP.
Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar rarrabe wutar lantarki ta Najeriya ta fada yajin aikin tun tsakar daren Asabar kuma ta tsinke dukkan layikanta da suke hade da jihar,
lamarin da ya bar jama’ar jihar cikin duhu. Wannan ya biyo bayan jan kunnen da kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa ta yi kuma ta bayyana cewa zata bi ayarin NLC wurin tafiya yajin aikin.