Firaministan rikon kwaryar Mali da gwamnatin kasar ta kafa wata tawaga ta musamman za ta yi mata garambawul, a dai dai lokacin da take fuskantar caccaka daga ‘yan adawa kan yadda sojoji suka mamaye mafi rinjayen mukamai.
A ranar Juma’a ne dai Firaministan kasar ta Mali Moctar Ouane yayi murabus, sai dai nan take gwamnatin rikon kwaryar shugaban kasa Bah Ndaw ke jagoranta ta sake nada shi kan mukamin, tare da dora mishi alhakin gudanar da garambawul ga gwamnatin.
A watan Agustan bara sojoji suka nada Moctar Ouane fira ministan Mali bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Kieta saboda gaza magance matsalolin kasar da yayi, ciki har da zanga-zangar in jinin gwamnati.
Bayan matsain lamba daga kasashen ketare ne kuma sojin na Mali suka kafa gwamnatin rikon kwarya da ta kunshi sojojin da farara hula da suka yi alkwarin za ta mikawa cikakkiyar gwamnatin farar hula muki bayan watanni 18.
Sai dai hakan bayan kawo karshen sukar tsare-tsaren sojojin da gamayyar ‘yan adawa karkashin kungiyar M5 ke yi, wadanda ko a makon jiya sai da suka nemi rushe gwamnatin rikon kwaryar.
A wani labarin na daban Firaministan Mali dake rikon kwarya Moukhtar Ouane, ya sanar da shirin gwamnati na soma tattaunawa da mayaka masu ikirarin jihadi da suka addabi sassan kasar musamman yankin arewaci.
Yayin ganawa da manema labarai a jiya Juma’a, Firaministan yace koda yake tattaunawar ba itace hanya tilo ta warware matsalar ta’addanci a Mali ba, za ta taimaka matuka wajen maido da zaman lafiyar kasar.
Kawo aynzu dai, Firaministan bai yi karin bayani kan wadanda za a wakilta jagorancin tattaunawar da mayakan masu ikirarin Jihadi ba.
A baya bayan nan Faransa dake taimakawa Mali wajen yakar masu tada kayar baya da dakaru dubu 5, tace bata goyi bayan shiga tattaunawa da ‘yan ta’adda ba, wadanda suka kauracewa yarjejeniyar sulhun shekarar 2015.
Kawo yanzu sojojin Faransa 55 suka rasa rayukansu a kasar ta Mali, yayin fafatawa da mayaka masu ikirarin Jihadi.
MALI