Mista femi adesina wanda shine mai baiwa shugaban kasa muhammadu buhari shawara kan lamurran kafofin sadarwa na zamani yayi a ranar alhamis yayi wani jriwaye inda a fakaice ya zargi sheikh ahmad mahmud gumi da cewa yana matukar son ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutanr.
Femi adesina ya wallafa cewa ”Ina son wannan lallabawar, kaima haka ko?” yana nufin yadda Dr. gumin ya dage a kan cewa lallai a bi ‘yan ta’addan a hankali domin fada dasu bazai kawo karshen matsalar tasu a ganin ganin Dr. Gumin.
Femi adesina ya maida martani a kan kiran da Gumi yayin na cewa a yafe wa ‘yan garkuwa da mutane kamar yadda aka yafe wa ‘yan naija delta, inda Adesina ya bayyana matsayar Gumi a matsayin tsantsar karya da daurewa ‘yan ta’addan baya.
Ranar litinin din data gabata ne dai Dakta Ahmad gumi ya bukaci gwamnatin tarayyar ta tabbatar bata shiga rikici da ‘yan ta’addan ba domin a ganin sa hakan bazai haifarwa da najeriya da mai ido ba.
Dakta Ahmad gumi yana da ra’ayin cewa dole a zauna da ‘yan ta’addan kuma cika musu muradan su sa’annan ayi sulhu dasu a kuma yafe musu duk laifukan da suka aikata, kama dagaa kisan kai, fyade, sata da dai sauran su.
Bayan wannan martani na femi adesina ma dai da yawan al’umma masu ta’ammuli da kafofin sada zumunta sun tofa albarkacin bakin su dangane da wannan bayani da Gumi, inda kusan gabadayan suke nuna rashin amincewar su da wannan ra’ayi na dakta gumi.
Lamarin har ta kai ga wani daga cikin masu ta’ammuli da kafar sada zumunta mai suna Isah Bn Isah ya wallafa a karkashin labarin ra’ayin gumi din da katsina online suka kawo ina ya rubuta, ”Allah gafarta malam cikin girmamawa da sunkuyar da kai, karya kake wallahi”
Sheikh gumi dai ba yau ya saba kawo ra’ayoyin wadanda ake ganin suna sabawa da hankali ba.