Gabanin bayyana sunayen ministocin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, masu ruwa da tsaki suna ci gaba da gabatar da jawabai da shawarwari da za su yi tasiri ga wanda shugaban kasa ya zaba a matsayin ministan Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).
Duk wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kokarin da ministocin FCT da suka shude suka yi na bunkasa birnin, ta fuskar manyan tituna da samar da ababen more rayuwa da bullo da sabbin tsare-tsare.
Daga cikin kungiyoyin masu ruwa da tsaki har da ’yan asalin Babban Birnin Tarayya Abuja wadanda suka yi imanin cewa wani minista daga cikinsu zai karfafi jam’iyya mai ta hanyar sama mata tagomashi.
Haka kuma masu ra’ayin samun wannan mukami na ministan Abuja akwai kungiyoyin siyasa daga yankin Arewa ta Tsakiya, musamman Jihar Neja da suke fatan samun tukuici saboda hobbasar da suka yi na ganin jam’iyyar ta kai gaci ta hanyar ba ta kuri’u mafi yawa a yankin, tare da hange tarihin cewa an yanki wani bangare mai yawa na babban birnin tarayya Abuja daga Jihar ta Neja.
Masu son ci gaba daga sashen kungiyoyi masu zaman kansu kuma suna kaunar ganin Shugaba Tinubu ya nada minista a babban birnin tarayya mai hangen nesa, da kuma karfin samar da tsarin sufuri na zamani, da kara bude wuraren raya kasa da samar da ababen more rayuwa da za su dace da al’ummar birnin.
Yawan jama’a yana kara matsin lamba ga sabuwar gwamnati akan lallai ta bullo da wasu sabbin hanyoyi na don bunkasa ababen more rayuwa gami da bude wasu gundumomi fiye da gwamnatocin da suka shude.
Festus Adebayo, wani masani ne a fannin harkokin gidaje kuma mai shirya taron baje kolin gidaje na Abuja, ya jaddada bukatar lallai gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Tinubu da FCTA hanzarta aiwatar da shirin nan na Abuja ‘Master Plan.
A cewar Adebayo, aiwatar da wannan shiri na da matukar muhimmanci ga shirin da aka tsara domin dorewar ci gaban Abuja, wanda aka amince da shi a matsayin daya daga cikin biranen da suka fi saurin habaka a duniya.
Da yake ganawa ta musamman da kafar LEADERSHIP Sunday a Abuja, masani kan harkar gidajen, ya jaddada bukatar sake tsara shirin sufuri a Abuja domin inganta zirga-zirgar al’umma.
Ya yi imanin cewa ingantaccen tsarin sufuri na da muhimmanci ga ci gaban birnin baki daya.
Makonni uku da suka gabata ne Adebayo ya yi wani tsokaci game da kwacen wasu filaye da aka yi a Abuja, lamarin da ya haifar da rashin daidaito a harkar zuba jarin gidaje.
Ya yi kira ga sabon Ministan Babban Birnin Tarayya zuwa da ya gabatar da ajandar magance wannan matsala, musamman ga ma’aikatan da suka yi ritaya wadanda ake zargin suna sayar da filaye ba tare da cikakkun bayanai ba kafin su bar ofis.
Kazalika ya ba da shawarar karfafa kotunan tafi-da-gidanka don magance matsalolin tsare-tsare na filaye a yankuna, yana mai jaddada bukatar yin karatun ta nutsu da kyakkyawan lissafi a lamarin.
Bugu da kari, ya yi nuni kan a gaggauta zartar da kudurin dokar kadarorin gidaje wato (Regulation and Debelopment) ta zama doka.
Babban abin da ‘yan asalin FCT suka fi ba wa fifiko shi ne, mayar da hankali kan siyasa domin ganin hakarsu ta cimma ruwa sun samu minstan Abuja.
Tsohon mai ba Tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Mallam Muhammad Bello shawara na musamman kan harkokin matasa, Mista Dabid, ya dora alhakin shan kayen da jam’iyyun siyasa masu mulki ke yi a Babban Birnin Tarayya Abuja kan nadin da aka saba yi wanda ba na dan asalin birnin tarayyar ba a matsayin minista.
Ya ce nada dan asalin Abuja a mukamin ministan babban birnin tarayya abu ne da suka dade suna fafutukar ganin an yi domin tabbatar da adalci da daidaito.
“Hakan da ake yi ba bisa ka’ida ba, kamar nuna karfa-karfa ne, kuma ba doka bace. Mun cancanta akan hakan domin muna biyayya ga doka domin ganin mun samu wanda aka nada da zai wakilce mu a majalisar ministoci.
Sai dai watakila ba lallai ne ministan da za a bamu ya zama ministan babban birnin tarayya ba, amma dai abin da muke ishara izuwa gare shi shi ne, ba mu ministan babban birnin tarayya zai zame wa jam’iyyar alheri sosai.
“Ya kamata gwamnati mai ci ta daidaita lamarin musamman a jam’iyyance.
Ita dai jam’iyya mai mulki ta sha wahala wajen ganin ta lashe zabe a Abuja, domin a kullum ana nada mutanen da ba su cancanta ba a matsayin ministocin babban birnin tarayya.
Ya kamata su nada dan asalin birnin a matsayin ministan su ga bambanci,” in ji shi.
Sai dai bisa ga dukkan alamu na wasu ‘yanlele ko wata kafa mai karfi da wadanda ake ba wa wannan kujera suke da ita daga ‘yan siyasa kamar dai yadda wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ba ke cewa tsohon gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ake sa ran zai bar kujerarsa ta Sanata ya zama ministan.
LEADERSHIP Sunday ta ruwaito cewa, tun a shekarar 1999 Jihar Nassarawa da Kogi ne kadai suka samar da karamin ministan yankin daga shiyyar duk da cewa yankin na da iyaka da wasu jihohin Arewa ta Tsakiya.
A tarihance, Jihar Neja, wadda ta mika mafi yawan yankunanta ga babban birnin kasar, ba ta taba samun da ko da karamin minista a yankin ba tun daga 1999 zuwa yau.
Wani mamba a majalisar zartarwa ta kasa na kungiyar ‘Arewa Consultatibe Forum’, Alhaji Babasule Bissalla (Sarkin Shanu Suleja) ya ce wannan bukata ta shiyya da musamman Jihar Neja ke da ita na samun da ministan babban birnin tarayya abu ne da ya jima.
Ya kara da samun wannan minista zai iya samar da hadin gwiwa ga garuruwan da ke makwabtaka da Suleja kan cewa ” Amma kuma za a iya jefa shi a kwandon shara idan bukatar ta wuce gona da iri duk da cewa babban birnin tarayya Abuja daga Jihar Neja aka yanko shi musamman ma Suleja,” in ji shi.
Shima da yake jawabi, a taron masu ruwa da tsaki, shugaban Matasan Arewa ta Tsakiya, Kwamared Mohammed Mohammed, cewa ya yi Arewa ta Tsakiya ta nuna goyon baya da gudunmawa matuka ga wannan gwamnati mai ci, kuma neman ministan babban birnin tarayya ga wannan yanki ba abu ne da za a ce bukata da za ya yi girma ba.
Ya ce musamman Jihar Neja ta sadaukar da fadin kasarta da kuma dukkan al’amuranta siyasarta, shi ya sa kungiyar ke neman mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Mohammed ya ce idan aka yi adalci, yankin na bukatar a ba shi kulawar da ta dace, don haka a ba Jihar Neja ministar babban birnin tarayya.
Kalmar nan ta “Buy before leabing office” tsohon ministan Abujan ya bayyana wasu nasarorin da ya samu, ta hanyoyin da ya bullo da su, wadanda ya gada kuma ya kammala da kuma samar da ababen more rayuwa a sabbin gundumomi.
Bello shi ne minista mafi dadewa a FCT wanda ya kwashe shekaru 8 yana mulki.
A ganawarsa ta karshe da ya yi kwana daya kafin ya bar ofis, ministan ya kaddamar da kwangilar aiki na injiniya karshe da zai lashe Naira biliyan 184 a gundumar Maitama II.
Gwamnatinsa ta kuma samar da kayayyakin aikin injiniya ga gundumar Wuye. Gundumar Wuye na daya daga cikin gundumomin da suka zama a mataki na biyu na babban birnin tarayya. Tana da jimlar fadi kimanin hekta 411 tare da yawan jama’a kusan 40,000.
Kwangilar samar da kayayyakin aikin injiniya ga gundumar Wuye na daya daga cikin ayyukan gundumomi da gwamnatin Bello ta gada.
Duk da haka, kafin zuwan wannan gwamnati, ayyuka sun tsaya cik saboda wasu makudan kudaden da ake bin su. Haka kuma akwai bukatar samar da gadar da ta hada Wuye da gundumar Wuse I, shiyya ta bakwai.
Gwamnatin da ta shude ta gaji wasu ayyuka daga gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan wanda Bala Mohammed a matsayin ministan babban birnin tarayya ta fara, kuma wadannan gwamnatin ta Buhari ta kammala su.
Wasu daga cikin ayyukan da wannan gwamnatin ta babban birnin tarayya Abuja ta gada karkashin jagorancin Bala Mohammed, kuma gwamnatin Bello ta kammala su ne; Kaduna zuwa Abuja da kuma zuwa babbar hanyar gwamnatin tarayya ta Lokoja (A2).
Haka kuma gwamnatin Bello ta gaji gadar gadar da ta hada titin jirgin kasa da kuma wasu sassa na titin da aka yi, wadanda aka kammala, an kaddamar da su, da kuma fara amfani da su.
Titin filin jirgin sama na farko da ya hada babban birnin tarayya (FCC) da babban titin Abuja zuwa Lokoja zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, shima yana daga cikin aikin da gwamnatin Bello ta gada daga daga gwamnatin Jonathan Goodlurck.
Shima aikin titin Goodluck Ebele Jonathan Way, an gaje shi daga daga gwamnatin Bala Muhammaed Tsohon Ministan Abuja wanda shi ne babban titin da ya hada babbar hanyar Abuja da Keffi.
Hukumar ta kusan kammala aikin gina Independence Abenue wanda ke a yankin Abuja ta Tsakiya a mataki na daya na birnin.
Gundumar tana da yankuna masu nau’ika kamar haka; yankin al’adu, yankin diflomasiyya, ma’aikatu, ofisoshin hadin gwiwar jihohi, ofisoshin kamfanoni, da ci gaban kasuwanci.
An yi aikin wasu yankuna misalin aikin da ya taso ne daga titin Circle Road da ke yankin Tree Arms Zone zuwa filin wasa na kasa tare da aikin Titin Independence.
Gwamnatin Muhammed Bello ta sha banban da sauran ministocin da suka gabata a Abuha, Adamu Aliero, wanda shugaba Umaru Yar’adua ya nada a watan Disambar 2008 ya yi watanni 16 kacal, watannin sun yi tasiri sosai saboda ayyukan ci gaban da ya yi sun canza fasalin FCT.
Aliero ya bayar da Naira biliyan 257 na kwangilar gina manyan tituna biyu; babbar hanyar Kubwa da titin Lugbe/Airport.
Kwangilolin sun hada da fadada hanyoyin zuwa tituna 10 da kuma gyaran hanyoyin da ake da su.
Duk manyan titunan biyu an kammala su ne daga hannun magajinsa a ofis, Gwamna Bala Mohammed na Bauchi.
Mohammed a nasa bangaren ya fara aikin hanyar Apo-Karshi wanda aka bai wa M/S Kakatar CE.
An iyakance aikin a cikin 2011, tare da lokacin kammala shi a watanni 20.