Sama da jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) Cadets ne suka kammala samun horo daga Sansanin horar da jami’an hukumar ‘yansanda (PMFTC), Ende-Hills, da ke jihar Nasarawa bayan daukan kwas na tsawon wata tara.
Jami’an sun samu horon ne a kan kwasa-kwasai guda hudu, masu mukamin mataimakan Insifekta 6 (DIC6), Maza 96 da kuma mata 19.
Da ya ke jawabi a wajen yayen, shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya ce, “Horon ya fara ne daga watan Disamban 2022, Maza 96 da mata 19 ne suka samu horon, hakan ya kaimu ga samun Jami’an Cadets 115 a cikin hukumar EFCC.”
Kazalika, ya ce an koyar da su kan bangaren shari’a, fafatawa da sauran muhimman bangarori gabanin su fara gudanar da aikansu.
Ya kalubalanci jami’an da cewa, “Aiki ne jaa a gabanku da ya shafi kasa, don haka ku yi aiki tukuru domin cigaban kasar nan.”
Shi ma da yake jawabi, mataimakin Kwamandan horo ta PMFTC, Mohammed Yakubu Nda, ya ce, “Cigaba da horar da jami’an EFCC a muhallinmu wani karin haske ne da ke nuna yadda ake da kyakkyawar alakar aiki tsakanin hukumar da ta ‘yansanda.
“Don haka a shirye muke mu cigaba da basu dama su yi kowani irin horo a cibiyarmu.”
A wani labarin na daban sabon shugaban karamar hukumar Karasuwa a jihar Yobe da aka nada kwanan nan, Honorable Lawan Gana Karasuwa ya rasu.
A wata sanarwar manema labarai dauke da sanya hannun darakta Janar kan harkokin yada labarai na ofishin gwamnan Jihar, Mamman Mohammed ya ce, Gana ya rasu ne a asibitin Gwamnatin tarayya (FMC) Nguru bayan gajeruwar rashin lafiyar da ta riske shi.
LEADERSHIP ta labarto cewa marigayin ya taba zama Shugaban riko na karamar hukumar Karasuwa na waya shida kafin gwamnan Jihar Mai Mala Buni ya sauke su.
Kazalika an sake nada shi a matsayin shugaban rikon kwanaki kalilan.
Yana daga cikin shugabannin riko 17 da gwamnan ya nada da za a rantsar da su a gobe Juma’a.
Wani abokinsa, Hon. Ado Adamu Bomboy, ya misalta marigayin a matsayin mutum mai kirki, kamala da dattako.