Watanni da dama da suka wuce, Adeoye Fawaz, ya kasance mara galihu a jihar Lagas inda yake kwana a karkashin gadar Oshodi
Matashin ya shahara ne bayan ya lashe gasar wasan ‘chess’ kuma nan take dai mutane suka mayar da hankali ga labarin yadda yake rayuwa.
A ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba, Fawaz yayi nasarar fita tare da daya daga cikin manyan attajiran Najeriya, Tony Elumelu.
Labarin Adeoye Fawaz, wani matashi dan Najeriya wanda ya bar yan uwansa a Ibadan don aiki a matsayin kwandasta a Lagas ya burge mutane da dama a soshiyal midiya.
Watanni da dama da suka shige, Fawaz ya lashe gasar wasan ‘chess’ wanda kungiyar wasan chess a unguwar matalauta karkashin Tunde Onakoya ta shirya.
Fawaz ya hadu da Elumel
A wata wallafa da Tunde ya wallafa a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba, ya wallafa wani hoton yaron tare da Biloniya Tony Elumelu. Ya rubuta:
“Kimanin shekara daya da ya wuce, Fawaz ya kasance kwandasta yana rayuwa a karkashin gadar Oshodi, a yau ya samu damar fita da shahararren biloniya a duniya. wannan shine yadda mafarki yake.”
Kalli wallafarsa a kasa:
Attajirin dan Najeriya da yayi farin cikin karbar bakuncin Fawaz da sauransu ya ce:
Jama’a sun yi martani
@Th_collins07 ya ce::
“Abu na farko na zama kwandasta sannan kasa da shekara daya, zan fara fita da attajiran biloniya, dadi.”
@Dehbbie3 ya ce:
“Kimanin shekara daya da ya shige, abun da Fawaz ya so mallaka shine biredi da wake.”
@FolorunsoAyoba3 ya ce:
“Babu abun da ya fi karfin Allah dan uwa. Allah ya yi amfani da kai wajen sauya rayuwar Fawaz. Na san shi a karkashin gadar Oshodi.”
@ThinqNaija ya ce:
“Ya kamata a tuntubi duk mutumin da yasa haka ta faru kan yadda za a gyara tsarin ilimi a Najeriya. Gyara-gyaren tunani da dabi’a sune ya kamata su zama sakamakon ilimi.”
KARA KARANTA WANNAN
Karin Bayani: Shahararren Mawakin Bishara Na Najeriya Ya Yanke Jiki, Ya Mutu A Gidansa A Legas
@uche_smallie ya ce:
“Wowww!! Wannan sauki akwai mamaki matuka! Jinjina gareka Tunde.
Ban samu kyautar Kirsimetina ba tukuna.”
A wani labarin, mun ji cewa wani matashi ya tashi kan dalibai a jami’ar Lagas bayan ya shiga makaranta da galelliyar motarsa kirar benz sabuwa gal.
Yadda motar ta tsaru ya matukar burge dalibai har sai da suka garzaya kusa da ita domin sanya albarka ta hanyar tabawa.
Source:Legithausa