Wata kotun majistare da ke zamanta a Fatakwal ta tura magoya bayan Atiku Abubakar zuwa gidan yari har sai 22 ga watan Maris.
Rundunar yan sanda ta gurfanar da mutanen ne a kotu kan zarginsu da zama yan kungiyar asiri bayan kama wasu wurin wani taro.
Wani lauya mazaunin birnin Fatakwal wanda ya ce ya halarci zaman shari’ar ya yi zargin rashin adalci yana mai zargin ana musgunawa magoya bayan Atiku ne saboda ba a samu matasan da wani makami ko barna ba.
Kotun majistare da ke zamanta a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, ta tsare a kalla mutum 20 da ake zargi da taro da mambobin kungiyar goyon bayan Atiku a gidan yari, rahoton The Punch.
An gurfanar da su a kotun ne kan zargin hadin baki, kasancewa cikin kungiyar asiri da yin taro ba bisa ka’ida ba.
Babban alkalin kotun, Collins Ali ya ke amincewa da bukatar beli da lauyan wadanda aka yi karar ya nema.
Ya kuma bada umurnin a tisa keyarsu zuwa gidan gyaran hali har zuwa ranar 22 ga watan Maris na 2023 kafin a duba yiwuwar bada su beli.
Akwai alamun rashin adalci a shari’ar, in ji lauya mazauin Fatakwal
Da ya ke magana da manema labarai bayan zaman kotun, wani lauya mazaunin Fatakwal, Victor Orokor, wanda ya saurari shari’ar ya soki rundunar yan sanda kan gurfanar da wadanda ake zargin, yana mai cewa ba bawa mutane ikon zaben wanda suke so.
Orokor ya ce: “A bangaren gwamnati ba kotu ba domin ita kotu za ta yi aiki ne da abin da aka kawo gabanta bisa doka. ”
Amma a bangaren hukunci, yan sanda, musamman kwamishinan yan sanda bisa alamu na hannun daman gwamna ne, ina ganin shari’ar akwai rashin gaskiya.
“Ana tsangwamar masu goyon bayan Atiku ne saboda ba a kama su da komai ba.
Babu lalata kaya. Ba su dauke da wani abu na laifi, ko kwalabe, ba a lalata motocci ba.
Yan kasa ne nagari. “Abin takaici ne mutane ba za su iya goyon bayan wanda suke so ba, muna son a bawa yan Ribas yanci su zabi wanda suke so.
Duk wanda ya yi nasara, za mu goyi bayansa a Ribas.”
Martanin yan sanda Kakakin yan sandan jihar Grace Iringe-Koko ta ce: “Yan sandan, a ranar 5 ga watan Fabrairun 2023 misalin karfe 1.30 na rana sun kama wasu mutum 32 a wani boyayyen wuri kan zargin zama mambobin kungiyar asiri. ”
Wannan ba shi da alaka da siyasa.
An binciki wadanda aka kama, an saki 12 cikinsu. Duk wadanda aka tarar ba su da laifi za a sake su, masu laifi kuma a kai su kotu.”
A wani rahoton, Helen Boco, tsohuwar yar takarar kujerar mataimakiyar gwamnan a zaben shekarar 2019 a jihar Cross Rivers a APC ta koma jam’iyyar PDP.
A cewar wani rahoto da Trinune Online ta wallafa, Boco ta sauya shekar ne yayin da ya rage kwana 49 a yi babban zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Source:LegitHausa