Faruk Adamu Aliyu ya bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba su fito da ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa ba.
‘Dan siyasar ya ce Asiwaju Bola Tinubu bai gama yanke shawara ba ne saboda yadda sha’anin kasar nan yake sarkakiya sosai.
Hon. Farouk Adamu Aliyu ya ce abin da za su duba shi ne cancanta, ba tare da la’akari da addinin abokin takarar Tinubu ba.
Farouk Adamu Aliyu wanda yana cikin kusoshin a jam’iyyar APC mai mulki, ya bayyana cewa ba addini za su yi la’akari da shi a zaben 2023 ba.
A wata hira da aka yi da Hon. Farouk Adamu Aliyu a Channels TV, tsohon ‘dan majalisar ya ce cancanta za a duba wajen tsaida abokin takarar Bola Tinubu.
Farouk Adamu Aliyu yake cewa ba a fitar da sunan ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a APC ba ne domin har yau Bola Tinubu bai kammala shawara ba.
Fitaccen ‘dan siyasar na jihar Jigawa ya shaidawa gidan talabijin da zarar an bada sanarwar wanda aka dauka, kowa zai gamsu an yi abin da ya kamata.
Ba batun addini ake yi ba a 2023 Aliyu wanda ya taba rike shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilan Najeriya ya ce APC ta na duba yadda za ta lashe zabe ne ba wai addinin ‘dan takara ba.
A ranar Lahadi, The Cable ta rahoto tsohon ‘dan takaran gwamnan ya ce duk wanda jam’iyya ta tsaida, za ayi bakin kokarin ganin an yi nasara a zaben 2023.
“Da zarar sunan ya fito, kowa zai yarda, kuma ya gamsu mun zabi wanda ya dace. Saboda haka, a kara mana lokaci kadan, za mu fito da shi.”
“Tsaida abokin takara ba abu mai wahala ba ne a wajen ‘dan takararmu (Bola Tinubu), sai dai saboda yadda kasar nan ta ke da wahalar sha’ani.”
“Za a fahimci abin da ya sa ake maganar tikitin Musulmi da Musulmi, Musulmi da Kirista da sauransu, an manta dole ne sai an lashe zabe tukun.”
“Mu na shawara, mu na da duba batun tikitin Musulmi da Musulmi da na Musulmi da Kirista, a matsayinmu na jam’iyya, ba batun addini ba ne.”
“Idan mun tsaida Musulmi-Musulmi, shikenan, za mu tabbata mu ci zabe. Idan Kirista aka kawo, za mu dage mu yi nasara, ba batun addini ba ne.”
Hon. Faruk Adamu Aliyu Tinubu ya na neman abokin takara Dazu kun ji labari Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yabawa kokarin da Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya taka wajen samun takarar shugaban kasa da ya yi a zaben APC.