Malamin jami’ar birnin Johannesburg a kasar Afirka ta kudu Farfesa Na’im Janah ya bayyana cewa Isra’ila tana hankoron ganin ta rusa alaka tsakanin Tarayayr Afirka da Falastinu, ta hanyar kutsawa cikin wannan tarayya.
Farfesa N’im ya ce babban abin da Isra’ila take bukata shi ne, ganin cewa ta rarraba kan kasashen Afirka mambobi a kunyiyar Tarayyar Afirka, domin tana da masaniya kan cewa kasashen Afirka da dama ba za su taba amincewa da ita a matsayin mamba a cikin kungiyar ba, ko da kuwa a matsayin mai sanya ido.
Wannan ne a cewarsa ya sanya ta bi wasu hanyoyi na yin amfani da kawayenta, ko kuma kasashen da suke biyayya ga turawa ido rufe wajen karbar ta a cikin kungiyar a matsayin mamba mai sanya ido.
Daga lokacin ne kuma kasashen da ba su amince da hakan ba suka nuna rashin gamsuwarsu da wannan mataki, kuma suka kalubalanci hakan a fili.
Ko shakka babu wannan batu ya kawo rashin fahimta tsakanin wasu kasashe da kuma bangaren zartarwa na kungiyar tarayyar Afirka, musamman ma kasashe irin su Aljeriya, Afirka ta kudu da mafi yawan kasashen larabawan Afirka in banda Sudan da Morocco, dukkaninsu sun nuna rashin amincewa da karbar Isra’ila a matsayin mamba a cikin kungiyar tarayyar afirka.
Alamu suna nuna ikirarin farfesa na’im yana da kamshin gaskiya domin an shaidu isra’ilan tana shige da ficen tabbatar da cewa ta samar da rashin fahimtar juna tsakanin kasashen afirka da kuma bangaren falasdinu wanda hakan ba karamin babban abin takaici bane duba da yadda ake fatan samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin kasashen afirka da sauran kasashen sauran nahiyoyin duniya.