Zuwa 22 ga watan Disambar 2023 ake sa ran sojojin Faransa da ke yaki da masu ikirarin jihadi a Nijar za su kammala fita daga kasar da ke Yammacin Afirka, kamar yadda sojojin na Faransa suka sanar a ranar Talata.
Sojojin da ke mulki a Nijar ne suka warware yarjejeniyar tsaro da ke tsakaninsu da na Faransar sakamakon yadda dangantaka ta kara tsami bayan juyin mulkin da aka yi wa Mohamed Bazoum a karshen watan Yuli.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da cewa sojojin na Faransa za su bar kasar zuwa karshen shekara, inda rukuni na farko za su soma ficewa daga kasar a watan Oktoba.
“Zuwa 22 ga watan Disamba, duka sojojin Faransa da kayayyakinsu sun bar Nijar lafiya,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Rundunar sojin ta bayyana cewa ana ci gaba da janye sojojin bisa tsari.
Kafar watsa labarai ta kasar Nijar ta ruwaito cewa zuwa yanzu sojojin Faransa 1,346 da kuma kashi 80 cikin 100 na kayayyakinsu sun bar kasar, inda sojojin da suka rage a yanzu 157 ne kacal.
Sojojin da ke mulki a Nijar a halin yanzu sun yi watsi da yarjejeniyoyin da gwamnatin kasar ta cimmawa da Kasashen Yamma karkashin mulkin Mohamed Bazoum inda suke kokarin kulla alaka mai karfi ta fuskar tsaro da tattalin arziki da makwabtansu na Mali da Burkina Faso.
Duka kasashen uku da ke yankin Sahel na yaki da kungiyoyin da ke ikirarin jihadi duka masu alaka da al-Qaeda.
Kasashen kungiyar ECOWAS duka sun amince a ranar Lahadi a Abuja kan ci gaba da saka takunkumi kan Nijar sakamakon juyin mulkin da aka yi a kasar.

Source: TRTHausa