Ministar Tsaron Faransa Florence Parly ta ce, dakarun kasar sun yi nasarar kashe wani dan kasar Mali mai ikirarin jihadi da ake zargi da hannu a kisan wasu Faransawa 2 ‘yan jarida a shekarar 2013.
Parly ta ce, dakarun Faransa da ke yankin Sahel sun yi nasarar kashe wasu ‘yan ta’adda 4 a wani samame da suka kai a arewacin Mali a ranar 5 ga watan Yuni, cikinsu har da Bayes Ag Bakabo, wanda shi ne aka fi zargi da kisan ‘yan jaridar gidan rediyon Faransa 2, Ghislaine Dupont da Claude Verlon.
Ministar tsaron ta ce, kisan nasa na alamta wani dako mai tsawo da aka yi, a game da gano wadanda suka aikata kisan ‘yan jaridar a shekarar 2013.
A garin Kidal da ke arewacin Mali ne aka kama wadannan ‘yan jarida 2, jim kadan bayan sun yi wata ganawa da jagoran ‘yan awaren Azbinawa a yankin.
Bayan ‘yan sa’o’i ne aka tsinci gawarwakinsu da alamun harbin bindiga, inda kungiyar Al-Qaeda ta yankin Maghreb ta dauki alhakin kisan, tana mai cewa matakinta yana a matsayin ramuwar gayya ce a kan shiga yaki da ta’addanci da Faransa ta yi a kasar a farkon shekarar.
Wani sakamakon bincike da Faransa ta gudanar ya nuna cewa, Bakabo ne ya tuka motar akori-kurar da aka yi amfani da ita wajen satar ‘yan jaridar 2.
A ranar Alhamis ne shugaba Emmanuel Macron ya sanar da rage yawan dakarun Faransa dubu 5 da100 da ke aiki a yankin Sahel.
SANARWAR FMM KAN KISAN KWAMANDAN DA YA KASHE ‘YAN JARIDAR RFI
Kafofin yada labaran Faransa na France Medias Monde sun bayyana samun labarin kisan Baye Ag Bakabo wanda ya kama da kuma kashe wakilan RFI guda 2, wato Ghislaine Duppont da Claude Verlon a ranar 2 ga watan Nuwambar shekarar 2013 a Kidal da ke Mali, kuma suna dakon binciken shari’a da ake ci gaba da yi a kan kashe ‘yan jaridar su guda 2 domin bayyana abin tashin hankalin da ya faru da zai kai ga kama ‘yayan kungiyar da kuma sauran kwamandodinsu da masu taimaka musu domin fuskantar shari’a.