Femi Fani-Kayode, tsohon minista, ya gana da Tinubu a ranar Juma’a, 19 ga watan Agusta a Abuja don shirin fara kamfen.
A cewarsa, babu wani dan takarar shugban kasa a jam’iyyun hamayya da zai iya kayar da Tinubu.
Tsohon sufurin jiragen sama kuma jigon jam’iyyar APC, Cif Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa shi da sauran mambobin jam’iyyar za su yi aiki don ganin Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasar jam’iyyar ya yi nasara a 2023.
Legit.ng ta rahoto cewa Fani-Kayode ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a 19 ga watan Agusta, a shafinsa na Twitter @realFFK, bayan shi da kakakin majalisar wakilai na tarayya, Femi Gbajabiamila sun yi taron sirri da Tinubu a Abuja.
Da ya ke magana kan taronsu da dan takarar na APC, Fani-Kayode ya ce sun tattauna abubuwa masu muhimmanci a taron, ya kara da cewa abubuwa masu kyau za su faru a Najeriya karkashin Tinubu a matsayin shugaban kasa.
APC a shirye ta ke ta fafata don tabbatar da nasarar Tinubu A wani sako mai kama da gugar zana ga jam’iyyun hamayya, tsohon ministan ya ce APC za ta hada kai domin tunkarar yakin da ke gabansu na tabbatar da nasarar Tinubu.
Ya wallafa a Twitter: “Na yi farin cikin samun damar tattaunawa da dan takarar shugaban kasar mu kuma babban jagora, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kakakin Majalisar Wakilai, tsohon abokina kuma dan uwa, Hon. Femi Gbajabiamila yan kwanaki da suka shude.
“Mun tattauna abubuwa masu muhimmanci a yayin taron kuma za mu hada kai don ganin nasarar babban jam’iyyarmu ta APC a zaben shugaban kasa da ke tafe.
Abubuwa masu kyau za su faru a Najeriya karkashin shugabancinsa. Mun gode wa Allah.”
A wani rahoton, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce kauracewa tikitin musulmi da musulmi yasa ya ki yarda Asiwaju Bola Tinubu ya yi masa mataimaki a zaben shekarar 2007, The Cable ta rahoto.
Atiku, wanda ya yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo mataki daga 1999 zuwa 2007, ne ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a ARISE TV a ranar Juma’a.
Source: LEGITHAUSA