Kungiyar NGF ta nuna cewa biyan tallafin man fetur da ake yi yana rage abin da ta ke samu daga FAAC.
Ana fuskantar karancin kudin da za a rabawa Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan hukumomi Gwamnonin jihohi sun ce idan gudumuwar NNPC ya cigaba da yin kasa, biyan albashi zai gagare su.
Kungiyar NGF ta gwamnonin Najeriya ta koka a game da yadda ake kashe makudan kudi duk wata da sunan ware tallafin man fetur a kasar nan.
Punch a wani rahoto da ta fitar a makon nan, ta ce kungiyar ta NGF ta ce kudin tallafin man fetur da ake biya, yana tasiri a kan karfin tattalin arzikin jihohi.
Gwamnonin kasar sun yi wannan bayani a karkashin lemarsu ta NGF, a wata wasika da suka aikawa kwamitin bincike da majalisar wakilan tarayya ta kafa.
Wannan kwamiti yana kokarin gano gaskiyar adadin men fetur da ake sha duk rana a Najeriya. NGF ta aikawa Majalisa takarda.
Shugabar sashen aiki da ‘yan majalisa, tsaro da zaman lafiya na kungiyar NGF, Fatima Usman Katsina ta aikawa kwamitin takarda a madadin Gwamnoni.
A ranar 1 ga watan Yuli Katsina ta fitar da takardar da aka yi wa take da ‘Abin da aka gano a game da shan fetur a Najeriya’ zuwa ga Hon. Abdulkadir Abdullahi. Gwamnonin Najeriya a Fadar Shugaban kasa.
Gwamnonin sun nusar da ‘yan majalisar tarayyar zuwa ga wani taron majalisar NEC da aka yi a Nuwamban 2021, inda aka tattauna a kan farashin man fetur.
Nasir El-Rufai ya jagoranci kwamitin da ya yi zama da NNPC a taron majalisar tattalin arziki, tare da Gwamnonin jihohi biyar da jami’an gwamnatin tarayya.
Tallafi na cin kaso mai tsoka a FAAC Jaridar take cewa gwamnonin su na kokawa ganin yadda NNPC bai sa komai a asusun hadaka na FAAC saboda biyan makudan kudi domin a rike farashin fetur.
A dalilin haka, abin da yake shigowa asusun jihohi ya yi kasan da biyan albashi sai an yi da gaske. Takardar ta ce lamarin yana ta kara yin kasa tun 2019, kuma alkaluma sun nuna kason da ake samu a daga mai da gas zai ragu da N3bn zuwa N4.4bn a 2022.
Kungiyar NGF ta bayyana cewa ya wajaba ‘yan majalisa da sauran hukuma su dauki mataki, idan har ba ayi wani abin da ya kamata, biyan albashi ba zai yiwu ba. Kudin sallar idi a Kaduna Ku na da labari kamfanin Kaduna State Market Development and Management Company ya ce gwamnati ta yafe karbar N500, 000 na wurin yin sallar idi a Kaduna.
Musulman Kaduna sun shafe sama da shekaru 60 su na yin sallar idi a farfajiyar Murtala Muhammad, wannan shekarar sai aka nemi su biya kudin yin salla.