Kungiyar tarayyar Turai EU ta sanar da aniyarta ta zuba jarin Euro sama da biliyan 150 a Africa nan da wasu shekaru masu zuwa a matsayin wani bangare na aniyar farko na shirin zuba jari mai suna Global Gateway, kamar yadda shugabar hukumar gudanarwar EU, Ursula von der Leyen, ta sanar a Dakar, babban birnin kasar Senegal.
Von der Leyen, ta yi wannan tsokaci ne a taron manema labarai na hadin gwiwa tare da shugaban kasar Senegal Macky Sall, sai dai ba ta yi wani karin haske game da batun shirin zuba jarin ba.
A cewarta, za a gudanar da taron dandalin hadin gwiwar EU da Africa a ranakun 17 zuwa 18 ga watan nan na Fabriuary a birnin Brussels, wanda shi ne kashin farko na shirin hadin gwiwar bunkasa tattalin arziki tsakanin bangarorin biyu, wanda zai gudana karkashin sabon shirin bunkasa zuba jari a fannin gina kayayyakin more rayuwa na Global Gateway.
Von der Layen ta ce, tabbas suna bukatar bangarorin masu zaman kansu, da kwararru da kuma jari mai karfi, kuma suna bukatar tsarin shugabanci a matakin koli.