Esther Wairimu ta shiga tashin hankali bayan an bar ta da dawainiyar yara hudu ita kadai sakamakon mutuwar aurenta.
Esther Wairimu ta zanta da manema labarai inda ta bada labarin yadda ta samu cikin tagwaye daga abokin mijinta yayin da take da aure a kanta.
Mahaifiyar yara hudun tace zata iya yin komai domin mayar da hannun agogo baya saboda yanzu ta zama uwa mara natsuwa.
Tun farkon Wairimu ta kasance mai walwala da farin ciki tare da kwazo ta yadda har makaranta ta mallaka a Naivasha.
Amma bayan shekaru da dama da aurenta, mijinta ya fada cin amanarta, lamarin da ya fara daga mata hankali.
“Na yi kokarin yi masa magana amma ya cigaba da komawa wurin matan banzan.
Akwai lokacin da yaro ne ke kokarin shiga balaga, ana bukatar ganin mijina amma shiru baya nan.
Na kira shi kuma na aika sako amma ba a samun shi,” ta sanar da Tuco a tattaunawa da suka yi.
A Wajen Daurin Aurensa A lokacin da Wairimu ke asibiti wurin haihuwarta ta biyu, mijinta na can yana shanawa da wata mace, kuma suka je wurinta tare.
“Bayan kamar minti biyar da suka yi a wurina a asibiti, na ji tana cewa rabin raina zo mu tafi.
Sun kasa boye maitarsu,” ta bada labari.
Wairimu ta sanar da yadda ta bukaci taimakon abokin mijinta kuma ya dinga tsayuwa tamkar mahaifi ga yaranta.
Tace bayan suna, ya cigaba da zuwa duba danta don tabbatar da cewa lafiyarsu kalau.
Yana bai wa yaronta shawara tamkar mahaifinsa.
“Ya kan taimaka min da abubuwan bukata na gida kuma babu dadewa muka samu kusanci.
Daga nan ne har na samu ciki.
Na sha mamaki da naje asibiti aka ce min tagwaye zan haifa.
Ina zan kai su? Na shiga damuwa kuma na fara tunanin gazawata a matsayin uwa.
Ban yi tsammanin zai taimaka wurin kula da yaran ba saboda babu abinda ke tsakaninmu.
Kamar in bayar da yaran,” Wairimu tace.
A wani labari na daban, wata amarya da angonta da suka rasa rayukansu shekaru 30 da suka gabata sun yi aure a wani gagarumin bikin kece-raini wanda ya samu halartar ‘yan uwansu da abokan arziki a Indiya.
Wani ma’abocin amfani da Twitter ‘dan kasar Indiya mai suna @anny_arun ne ya bada labarin yadda auren ya kasance.
Ya yi bayanin cewa, a al’adarsu idan mutum ya mutu yana karami, iyalan mamacin na iya nemo wani wanda ya rasu yana karami ta yadda za a yi musu aure.
Source:hausalegitng