An zargi Godwin Emefiele da kai hari kan ‘yan siyasa da gabatar da dokar kayyade kudin da za a iya cirewa daga banki.
A cewar Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, gwamnan na CBN na yin hakan ne don ya gaza samun tikitin takarar shugaban kasa na APC.
Hakazalika, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi garambawul ka kundin tsarin mulki don mayar da Najeriya tarayya ta ainihi.
A wani abu da za a iya kwatantawa da cigaba mai ban mamaki, Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya yi babban zargi kan gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele.
A cewarsa, Emiefiele yana kai wa yan siyasa hari ne da dokar kayyade adadin kudin da za a iya cire wa daga banki, Punch ta rahoto.
Har wa yau, Gwamna Finitiri ya ce an kawo dokar ne jim kadan bayan rashin nasara da Emefiele yayi a siyasa da ta zo karshe cikin gaggawa, kuma hakan ramuwar gayya ne saboda yana son tsananta talauci a cikin al’umma.
Ya ce: “Me ke kawo talauci? Tsare-tsaren kudi. Duba wanda babban bankin kasa ke shirin aiwatarwa wanda ka iya kara jefa kasar cikin talauci,
Babu wanda ke cewa kada a sauya tattalin arziki zuwa mara amfani da tsabar kudi ba.
“A dauki lokaci a yi shi dalla-dalla. Kada mu yi kamar wasu mutane sun so zama yan siyasa amma ba su samu dama ba, sannan su yi amfani da ofishinsu don hukunta yan siyasa.”
Bugu da kari, Fintiri ya sake jadada kira ga cewa a mayar da kasar ta zama tarayya na ainihi.
Ya kuma ce akwai bukatar a sauya tsarin fasalin kasar ta yadda jihohi da kananan hukumomi za su rika cin gashin kansu.
gefe guda, Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, ya ce babu alamun yin watsi da aiwatar da sabuwar dokar kayyade cire kudi da aka kawo.
Gwamnan na CBN zai bayyana a gaban majalisar tarayya don amsa tambayoyi kan sabuwar dokar a ranar Alhamis 8 ga watan Disamba, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Emefiele ya ce tun a shekara 2012 ya fara shigo da tsarin rage amfani da tsabar takardan kudi amma aka jinkirta har sai an samar da wasu kafafen hada-hadan kudin a kasar.