An sake fuskanci wani tsaiko a shirin gurfanar da gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) da aka dakatar, Godwin Emefiele a gaban kotu, dangane da zargin karkatar da naira biliyan 6.9.
Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ba ta lissafa shari’ar da ake yi wa Emefiele cikin shari’un da za ta saurara yau Laraba ba.
Juyin Mulki: PRP Ta Bukaci ECOWAS Da Ta Rungumi Matakin Sulhu Da Sojojin Nijar
Sake Bude Sansanin NYSC Na Borno Ya Tabbatar Da Zaman Lafiya Ya Samu A Jihar – Zulum
Lauyoyin Emefiele da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), wadanda su ne masu gabatar da kara, ba su halarci zaman kotun ba,
Ba a dai bayar da dalilin da ya sa shari’ar ba ta cikin jerin shari’un da za a saurara a kotun ba.
DSS dai ba ta mayar da martani game da lamarin ba.
A ranar Alhamis din da ta gabata, Emefiele ya bayyana a kotun amma kotun ta dage karar saboda Sa’adatu Yaro, wata ma’aikaciyar babban bankin, kuma wadda ke fuskantar tuhuma tare da Emefiele ba ta bayyana a kotun ba.
Wannan ne ya sa mai shari’a Hamza Mu’azu, ya dage sauraren karar zuwa ranar 23 ga watan Agusta.
Yaro da Emefiele suna fuskantar tuhume-tuhume 20 daga DSS, da suka hada da zamba da hadin baki da bayar da cin hanci da rashawa ga abokan hulda.
Ana tuhumar Mista Emefiele da bai wa Sa’adatu Yaro, wadda ta ke darakta a April 1616 Investment Ltd, wani kamfani da ake zargi da alaka da lamarin.
Source: LEADERSHIPHAUSA