Elon Musk, attajirin duniya kuma sabon mammalakin dandalin Twitter ya ce akwai yiwuwar dawo da shafukan wasu da aka toshe Wannan na cikin sabbin sauye-sauyen da Musk ke yi ne bayan ya siya kamfanin ya kuma kori wasu daga cikin manyan shugabannin kamfanin.
A cikin fitattun mutanen da aka toshe wa shafin Twitter, akwai Donald Trump, tsohon shugaban Amurka wanda ya ce ba zai dawo ba.
Sabon mammalakin Twitter, Elon Musk a ranar Laraba ya ce nan da makonni kadan za a bude shafukan mutanen da aka dakatar da su kamar tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, Channels TV ta rahoto.
Masu amfani da Twitter suna sa ido su gani ko Musk zai bude shafin Trump da aka dakatar saboda tunzura mutane yin boren ranar 6 ga watan Janairu a ginin majalisar dokoki a Washington.
Dawo da irin wadannan shafukan da aka toshe saboda saba dokokin dandalin zai iya zama manuniya kan inda dandalin zai fuskanta a karkashin shugabancin Musk, wanda ke bayyana kansa a matsayin ‘mai son ganin kowa ya samu yancin tofa albarkacin bakinsa’.
Amma a ranar Laraba, attajirin dan Afirka ta Kudu ya ce za a jira na wani lokaci kafin ganin matakin da zai dauka.
Ya wallafa a Twitter cewa: “Twitter ba zai bude shafin duk wanda aka rufe saboda saba dokokin Twitter ba har sai mun samu sahihin hanyar yin hakan, wanda zai dauki yan makonni nan gaba.”
Trump ya ce ba zai dawo Twitter ba Tunda Musk ya kammala cinikin Twitter a makon da ya gabata, Trump ya nuna alamun zai cigaba da amfani da dandalinsa na Truth Social a maimakon dawowa Twitter.
Amma wasu masu nazarin tsarin siyasa suna ganin zai yi wahala Trump ya ki dawowa dandalin na Twitter idan an bude shafinsa, duba da cewa yana da mabiya da karfin fada a ji sosai.
Kamfanin Twitter, a ranar Litinin ta tabbatar da cewa za ta sayarwa attajirin duniya Elon Musk kan kudi Dallar Amurka Biliyan 44, The Punch ta rahoto.
Sayar da kamfanin abin mamaki ne duba da cewa da farko mambobin kwamitin kamfanin sun ki amincewa Musk ya siya kamfanin dandalin sadarwar.