Sauye-sauyen da Elon Musk ke ta yi wa Twitter kullum cigaba yake bayan da ya lale $44 biliyan ya siya kamfanin a watanni biyu da suka wuce.
Garambawul din baya-bayan nan shi ne na gyaran ofisoshi da aka yi wa kamfanin wanda an yi shi ne don kara karfin guiwa ga ma’aikata.
An sauya ofisoshin tare da yi musu kwalliya suka koma tamkar dakunan otal wanda aka zubawa zannuwan gado da durowoyi.
Elon Musk ya kammala gyara tare da kimtsa ofisoshin Twitter wanda hakan ya tayar da maganganu.
Bayan Elon Musk ya kammala ciniki tare da siyan kamfanin kan $44 biliyan, ya fatattaki manyan shugabannin kamfanin da wasu ma’aikata.
Ga ma’aikatan da suka ragu, CNN ta rahoto cewa Musk ya aike musu da sakon Imel kan cewa dole su dage su yi aiki tukuru ko kuma su bar kamfaninsa.
“Domin cigaba, da gina sabuwar Twitter 2.0 da zata nasara a gogayya da gasar duniya, za mu bukaci aiki tukuru.”
Musk ya rubuta a wata takarda
“Wannan yana nufin aiki na tsawon awanni babu sassauci.
Aiki tukuru na wuce tsara ne kadai zai tabbatar da mafita.”
Musk ya mayar da ofisoshin Twitter zuwa otal Domin tabbatar da an yi abinda yake so na aiki tukuru, Musk ya kirkiro dakunan bacci a ofisoshin.
Dakunan baccin kamar yadda Bloomberg ya rahoto, zasu dauka ma’aikata daga Tesla da sauran kasuwancin Musk wadanda aka shigo dasu don aiki a Twitter, “wasu daga cikinsu suna yin doguwar tafiya don taruka a Twitter.”
Wani hoto da BBC News ta samu ya nuna daki da gidaje biyu, wadurob da takalma.
BBC har ila yau ta fitar da hotunan kujeru a Twitter wadanda ake amfani dasu matsayin gadaje.
Wani dakin taro ya mallaki agogon tashi daga bacci da kuma wani hoto da aka saka saman gado.
“Ya yi kama da dakin otal.” – daya daga cikin tsofaffin ma’aikatan kamfanin yace.
Sun kara da cewa Musk yana kwana sau da yawa a hedkwatar Twitter dake San Francisco.
Musk yace gadajen zasu taimakawa ma’aikata hutawa idan sun gaji.
Wani tsohon ma’aikacin Twitter ya sanarwa BBC cewa sabon mai kamfanin Twitter din zama ya koma yi a hedkwatar kamfanin tun baya da ya siya kamfanin.
Elon Musk ya siya Twitter
A wani labari na daban, hamshakin mai kudin duniya, Elon Musk, ya siya kamfanin Twitter kan $44 biliyan.
Bayan siyan kamfanin, ya bayyana cewa “tsuntsuwar ta samu ‘yanci” a wallafar da yayi.