A yau Asabar, sama da mutum 749,000 ne a jihar Ekiti za su yanke hukuncin wanda zai gaji Gwamna Kayode Fayemi a zaben da babu shakka za a matukar fafatawa.
Manyan masu taka rawar gani su ne Dr. Fayemi, gwamna mai ci yanzu da tsohon gwamnan jihar, Niyi Adebayo, wanda shi ne ke jagorantar kamfen din ‘dan takarar APC, Biodun Oyebanji.
Wani tsohon gwamna, Ayodele Fayose, yana bangaren ‘dan takarar PDP, Bisi Kolawole, yayin da ‘dan takarar SDP, Segun Oni, shima tsohon gwamna ne.
Hakazalika, akwai ‘yan takarar ADC, Wole Oluyede, wanda cikakken likita ne; na YPP shi ne Debo Ajayi da na ADP, Adeynka Alli, matashin ma’aikacin banki.
A dukkan jam’iyyun siyasa 16 da suka tsayar da ‘yan takara a zaben gwamnonin Ekiti, banda jam’iyyun APC, PDP da SDP, ‘yan takarar sun ce nasara suka fito samu ba takara ba kawai.
Biodun Oyebanji yana zaga wa rumfunan zabe tare da matarsa Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben na Ekiti, Biodun Oyebanji, a halin yanzu yana zaga wa rumfunan zabe tare da matarsa.
Ana tantance masu zabe tare da jefa kuri’a a karamar hukumar Emure Zabe na tafiya yadda ya kamata a karamar hukumar Emure, Gunduma ta 5, rumfar zabe ta 10.
Na’urorin tantance masu zabe suna aiki ba matsala a lokacin wallafa wannan rahoton.
Ina da tabbacin nine zan lashe zabe – Oyebanji Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Biodun Oyebanji, ya nuna karfin gwiwar cewa shine zai lashe zaben na jihar Ekiti wanda ke kan gudana a yanzu haka.
Oyebanji ya bayyana hakan ne bayan ya kada kuri’arsa. 10:41 Safiya Bidiyon tsohuwa mai shekaru 105 tana kwasar rawa bayan kada kuri’a.
A rumfar zabe mai lamba 006 dake Ofaki a karamar hukumar Ido-Osi ta jihar Ekiti, wata tsohuwa mai shekaru 105 ta kwashi rawa bayan ta kada kuri’a cike da farin ciki.
Ekiti jihar Farfesoshi ce, ba za mu karba cin hanci ba, Masu Kada Kuri’a Yayin da ake tsaka da kada kuri’u a rumfunan zabe a jihar ekiti, wasu masu kada kuri’a sun tabbatar da cewa ba za su karba cin hanci ba.
A cewarsu, jihar Ekiti jiha ce ta fafesoshi ba jahilai ba. Don haka babu ruwansu da rashawa. 10:10 Safiya Dan takarar PDP, Bisi Kolawole, ya kada kuri’arsa.
Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, Bisi Kolawole, ya kada kuri’arsa a mazabarsa ta 001, Ward 8, Efon VIII, Ojodi 1, jaridar Punch ta rahoto.
Gwamna Kayode Fayemi ya isa mazabarsa domin kada kuri’a Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya isa mazabarsa domin kada kuri’arsa a zaben gwamnan jihar da ke gudana a yanzu haka.
Masu zabe sun fara fita rumfunar zabensu domin ganin ba a barsu a baya ba.
A rumfar zabe ta 003, ward 06, Ikogosi, Ekiti ta yamma, an gano masu zabe zaune suna jiran jami’an zaben su bayar da umurnin fara shirin.
Hakazalika a rumfa ta 10, ward 4, Ijigbo, Ado Ekiti, an gano wasu dattawa mata da suka fito don kada kuri’a.
A cewarsu: “Mun rigada mun ga sunayenmu a cikin jerin wadanda za su kada kuri’a. mun shirya sauke hakkin mu na zabar wanda muke muradi.”
An fara tantance masu zabe da kada kuri’a a karamar hukumar Ado An fara tantance masu zabe da kada kuri misalin karfe 8.30 na safe a rumfar zabe ta 002, gunduma ta 10, karamar hukumar Ado.
INEC ta sanar da lokacin fara zabe da kuma lokacin kammalawa Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bayyana cewa za a fara tantance masu zabe da kada kuri’a da misalin karfe 8:30 na safe sannan a rufe da karfe 2:30 na rana. Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter, INEC ta ce duk mai rijistan zabe da ya shiga layi kafin karfe 2:30 na rana za a tantance shi don ya kada kuri’a, amma duk wanda ya zo bayan 2:30 na rana ba za a bari ya shiga layin ba.
7:17 Safiya An rarraba jami’an INEC zuwa rumfunan zabe An rarrabe jami’an INEC tare da kayan aikinsu zuwa rumfunan zabe a kananan hukumomin Ikole ta Yamma, Ijero da Irepodun/Ifelodun da karfe 6:30 na safiyar yau.
An tsaurara matakan tsaro a fadin jihar Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an tsaurara matakan tsaro a jihar ta Ekiti yayin da jam’iyyun siyasa ke fafatawa wajen neman kuri’u a zaben gwamnan da za a yi.
Yadda Ake Fafatawa a Zaben Gwamnan Jihar Ekiti Hoto: Segun Oni Asali: UGC Kasance mutumin farko da zai samu labarai da duminsu daga Babban Editanmu.