Hukumar EFCC ta bayyana yin gwanjon motocin da ta kwace daga hannun mutanen da ake zargi da rashawa a kasar nan.
Hukumar za ta yi kwanaki biyu ne tana wannan aikin kamar yadda dokar kafa ta ya tanada.
EFCC na ci gaba da aikin bankado badakala, ta kame wani matashi da laifin damfara wata mata ‘yar kasar Burtaniya.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a jihar Legas ya yi gwanjon motoci 435 da ta kwace a hannun jama’a daidai dokar kafa hukumar na 2004.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Wilson Uwujaren ya fitar, an ce hukumar ta fara aikin gwanjon motocin ne a jihar Legas a ranar 6 ga watan Disamba, kuma za ta yi hakan a sauran cibiyoyin ta.
A cewarta, za a yi aikin ne cikin tsanaki tare da sanya idon ‘yan kasa, kuma za a gama nan da ranar Alhamis, 8 ga watan Disamban bana, Vanguard ta ruwaito.
Hukumar ta ce, za a iya samun kayayyakin da za ta gwanjatar a wurare kamar haka: 40, titin Bourdillo, Ikoyi, Legas 15A titin Awolowo, Ikoyi, Legas,14 titin Cameroon Road, Ikoyi Legas da CVU Obalende, Ikoyi, Legas.
Jaridar The Nation ta yada wasu hotunan yadda aka gudanar da gwanjon.
Ana gudanar da gwanjon cikin tsanaki:
Hukumar ta kuma yi godiya ga daukacin al’umma da suka ba da hadin kai wajen gudanar da wannan aikin.
Hakazalika, hukumar ta godewa rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin da aka gayyata domin tabbatar da yin wannan aiki na gwanjo cikin kwanciyar rai.
“Ba Zaku Iya Kashe Rai Ba” FG Ta Umarci a Sauya Wasu Jami’ai Daga Gidan Yari
A tun farko hukumar ta sanar da yin gwanjon motocin da ta kwace a hannun wadanda ake zargi da rashawa da sace kudaden gwamnati.
Hukumar EFCC na ci gaba da aikin kamowa da gurfanar da wadanda ake zargi da yin almundahana a fadin kasar nan.
An kamo wani matashin da ya damfari wata mata ‘yar Burtaniya
A wani labarin kuma, hukumar ta EFCC ta kamo wani matashi da tace ya yi ruwa ya yi tsaki wajen kwace kudin wata mata ‘yar Burtaniya.
A cewar EFCC, Endurance ya lallabi matar ta tura masa Bitcoin da takardun kyauta, inda ya ci ya kai £450,000.
Abin da ya ba da mamaki shine, matashin ya ce shekarunsa 19 ne kacal.
EFCC na ci gaba da bincike kafin gurfanar dashi.