Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta kama tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari dangane da binciken da ake yiwa Akanta Janar na kasa Ahmed Idris saboda zargin karkata kudin da ya kai naira biliyan 80.
Kakakin hukumar Wilson Uwajiram ya tabbatar da kama tsohon gwamnan.
Tun 16 ga watan Mayu EFCC ta kama Akanta Janar na Najeriya Ahmed Idris bisa zarginsa da almundahana ta naira biliyan 80.
A wani labarin mai kama da wannan tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya jagoranci magoya bayan sa na Jam’iyyar APC dake mulkin Najeriya domin sauya sheka zuwa Jam’iyyar adawa ta PDP saboda abinda suka kira rashin adalcin da aka nuna musu.
Yari wanda ya taka rawa wajen hada Jam’iyyar AC da ANPP da APGA domin rikidewa a kafa Jam’iyyar APC yace shugabannin Jam’iyyar ta kasa ba suyi musu adalci ba tun daga lokacin zaben shekarar 2019 wajen haifar da matsalar da ta sanya karbe kujerun da suka lashe domin baiwa PDP a lokacin, wadanda suka hada da ta kujerar gwamna da ‘Yan majalisun Tarayya da na Jihohi
Tsohon gwamna yace bayan matsalar da aka samu a Jihar Zamfara, sai kuma jam’iyyar su ta APC ta mikawa Gwamna Matawalle ragamar jagorancin ta lokacin da ya sauya sheka daga PDP zuwa cikin ta, matakin da ya nuna rashin la’akari da rawar da suka taka wajen killace ‘yayan jam’iyyar ta su wuri guda duk da matsalolin da suka fuskanta.
Yari yace lura da wannan da kuma rashin adalcin da aka yiwa magoya bayan su a matakai daban daban, sun yanke hukuncin sauya sheka zuwa jam’iyyar da za’a mutunta su.
Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, Kanar Bala Mande ya tabbatar da sauya shekar a taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar da akayi a Gusau.
Kanar Mande yace sun cimma matsaya a tsakanin su akan yadda za’a habaka Jam’iyyar wajen aiki tare da sabbin ‘yayan ta, yayin da ake shirin bikin karba su nan gaba kadan.