ECOWAS Ta Yi Nazari Kan Takunkuman Da Ta Kakaba Wa Kasashe Mambobinta Da Juyin Mulki Ya Shafa.
Shugabannin kasashen yammacin Afirka sun gana a ranar jiya Lahadi a birnin Accra babban birnin kasar Ghana, domin duba takunkuman da suka kakaba wa kasashe uku daga cikin mambobin kungiyar da sojoji suka yi juyi mulki.
Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS sun hallara domin tantance kokarin da ake yi na tabbatar da jadawalin lokaci da lamuni na maido da mulkin farar hula a Mali, Guinea da Burkina Faso.
Da yake bude taron kolin na ranar Lahadi, shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya ce kungiyar mai mambobi 15 ta kuduri aniyar tallafawa kasashen uku wajen dawo da tsarin dimokuradiyya, kuma za su dauki matakin da ya dace bayan sauraron rahotannin ci gaban da suka samu.
Shugabannin na ECOWAS sun cimma matsaya kan soke takukunman tattalin arziki da kasuwanci da aka kakaba wa kasar Mali, haka nan kuma an cimma matsaya tare da mahukuntan soji na Burkian Faso kan mika mulki ga hannun farar hula a cikin shekaru biyu, maimakon shekaru uku, tare da sakin Roch Marc Christian Kabore tsohon Shugaban kasar da sojojin suke tsare da shi.
Sojoji sun yi juyin mulki a kasar Mali a cikin watan Agustan 2020 da Mayu 2021, sai Guinea a watan Satumban 2021, sai Burkina Faso kuma a watan Janairu.
A watan Janairu ne kungiyar ECOWAS ta kakaba wa Mali takunkumin kasuwanci da kudi bayan da gwamnatin sojan kasar ta kaddamar da wani shiri na mulki na tsawon shekaru biyar.