Kungiyar Ecowas ta kuma bukaci sojoji su gaggauta sakin hambararren shugaba Farfesa Alpha Conde, tare da yanke shawarar tura tawaga ta musamman zuwa birnin Conakry don ganawa da sojojin da suka yi wannan juyin mulki a wannan Alhamis.
A lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron a jiya, shugaban riko na kungiyar ta Ecowas wato shugaban Ghana Nana Akufo-Ado, ya bayyana juyin mulkin da cewa, ya saba wa dokokin kare dimokuradiyya da kyakkyawan jagoranci da kungiyar ta shimfida.
Jami’an tsaron Kamaru sun tsare wasu mambobin wata kungiyar tawayen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da suka shigo Ngaudere dake jihar Adamawan kasar, inda suke kokarin aikata ayyukan garkuwa da mutane.
Kwamandan rundunar Jandarmomin na jihar Adamawa, Kanal Jean Pierre Kagombe Keffiene yayin zantawa da manema labarai dangane da kamen, yace bayan nasarar cafke mahara biyu, suka samu damar kame wasu karin maharan da masu taimaka musu guda 4.
A cewar jami’in mayakan ‘yan tawayen da suka shigo kasar ta Kamaru ta hanyar amfani da wasu takardun bogi, sun kasance cikin kungoyin ‘yan tawayen da suka hana gwamnatin shugaba Faustin Arkange Touadera a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sakat tun a shekarar 2015, tare da haddasa yakin basasar da yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane.