Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ba shi da cikakken tsari kan yadda za a magance matsalar durkushewar darajar Naira akan kudaden waje, lamarin da ya yi illa ga tattalin arzikin Nijeriya.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani martani da ya mayar kan taron da Tinubu ya yi a ranar Alhamis din da ta gabata da gwamnoni da masu ruwa da tsaki domin magance matsalar canjin kudaden waje da kuma matsalar tabarbarewar tattalin arzikin Nijeriya.
Atiku ya bayyana cewa, a lokacin da gwamnati ta amince da amsar shawarwari na gari, ta tsunduma kan shawo kan kalubalen tsaro, ta toshe hanyoyin alfarma da ke haifar da cin hanci da rashawa kuma ta dakile yawan amso bashi daga kasashen waje, daga nan ne tattalin arzikin Nijeriya zai sake ci gaba da habaka.
Atiku ya ce, Tinubu ya gaza wajen nuna wani ingataccen matakin da gwamnatinsa ke dauka na shawo kan kalubalen tsaro, tsadar rayuwa, durkushewar darajar Naira da talauci da ke addabar kasar.
Dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023 ya ce, kuskuren manufofin Tinubu na ci gaba da haifar da damuwa ga tattalin arziki kuma “Bai dace, a zura ido ana kallonsa ba, babu mai fada masaG askiya”
Source: LEADERSHIPHAUSA