Abun jira a gani shine shin Mallam Abdul-Jabbar zai daukaka kara ko kuma zai hakura da wannan hukuncin da aka yanke masa, tattare da cewa DSS sun damke babban almajirin sa.
Daga cikin Hukuncin da alkali yayi yau har da batun sanya karatuttukansa a gidajen radio da talabijin da kafafen sadarwa na zamani.
Wannan dai na zuwa ne bayan da aka shafe sama da shekara guda ana gudanar da shari’ar ta sa.
A dokokin da jami’an tsaro suka sa a kwai hana jama’ar gari ko dai-daiku zuwa jin shari’ar ko zuwa sauararn karar, ciki kuwa harda mabiyan ko wanne bangare na mallam Abduljabbar da jama’ar gari sabida gudun tarzoma.
To sai dai jami’an tsaron farin kaya DSS, sun damke dalibin malam Abdulj-Jabbar mai suna Saifullahi Satatima, sabida zarginsa da zuwa harabar kotun ba tare da an gayyaceshi ba.
AbdulJabbar Kabara: Abubuwan da suka faru aka yanke masa hukuncin kisa Wakilin legit.ng Hausa ya ga lokacin da jami’an tsaron sukai gaba da shi, inda suka sa shi a motarsu kirar Hayis fara wanda gilasanta a rufe suke da bakin leda.
Saifullahi dai babba ne cikin manyan almajiran Abdul-Jabbar, hasali ma dai shine limamin dayan masallacin da kotu ta bada umarnin a rufeshi.
Yana da ga cikin abinda da mai shari’a Sarkin yola yace game da batun Abdul-Jabbar, yace ya yanke wannan hukuncin ne dan ya zama izina ga wanda yake so ya aikiata wani abu makamankin haka.
Mai shari’ar na fadin hakan ne yayin da yake yanke hukuncin shari’ar Abdul-Jabbar wanda aka kammalata.
Kamar yadda Legit.ng Hausa ta rawaito Mallam Abudul-Jabbar Nasiru Kabara yana da masallatai guda biyu da yake gabatar da karatuttukansa a ciki daya shine wanda yake limanci na filin mushe, dayan kuma yana sabuwar gandu ne, kuma shine masallacin da Saifullahi yake Limanci.
A Wanne Hali Daliban Abdul-Jabbar Suke?
Shekara daya da kusan wata takwas kenan da rufe masallaci hadi da makarantar Abdul-jabbar tun gabannin fara tirka-tirkar muqabala tsakaninsa da malamai.
Da dai kafin rufe masallacin ya zama cibiyar da su Abdul-jabbar suke gudanar da wa’azuzzkansu da kuma lakcoci.