Dole ne sojoji su koma bariki – CISLAC.
Cibiyar kare hakkin jama’a ta Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC) a karshen mako a Legas ta bukaci gwamnatin tarayya da ta janye sojoji daga ci gaba da gudanar da ayyukan tsaron cikin gida domin kare martabar sojoji.
Cibiyar ta ce kiran ya zama wajibi ne biyo bayan karuwar almundahana da cin zarafi da sojoji ke yiwa mutane a lokacin gudanar da ayyukan tsaro daban-daban a fadin kasar.
Babban Darakta na CISLAC, Auwal Ibrahim Musa (Rafsanjani) ya ce idan aka dawo da su bariki zai rage zaluncin da sojoji ke yi wa fararen hula, wadanda a cewarsa, wuce gona da iri ne.