Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kai karar majalisar dokokin jihar kan zargin gwamnatisa da karkatar da Naira biliyan 432.
Majalisar ta yi zargin cewa ya yi amfani da Naira biliyan 432 ba bisa ka’ida ba a tsawon wa’adinsa na shekaru takwas, wanda ya hakan ya jefa jihar cikin kangin bashi.
Lauyan El-Rufai, Abdulhakeem Mustapha, ya shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Laraba.
Lauyan ya kalubalanci rahoton majalisar da ya zargi El-Rufai da karkatar da dukiyar jama’ar jihar.
Kwamitin majalisar dokokin jihar, ya yi bincike game da wasu kudade, bashi da kwangiloli da El-Rufai ya bayar a lokacin mulkinsa.
Kakakin El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya ce har yanzu ba su samu rahoton ba amma za su yi martani da zarar sun samu rahoton.
Ya jaddada cewar gwamnatin El-Rufai, ta yi aiki bisa gaskiya, inda ya ce sun yi watsi da ikirarin majalisar dokokin.
Leadership Hausa
Gwamnatin Sakkwato Na Ci Gaba Da Shirin Tsige Sarkin Musulmi – MURIC
by Sadiq 9 seconds ago
Gwamnatin Sakkwato Na Ci Gaba Da Shirin Tsige Sarkin Musulmi – MURIC
Duk da cewa gwamnatin Jihar Sakkwato ta musanta shirin tsige Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), ta ce har yanzu gwamnatin na ci gaba da shirin tsige Sarkin.
A wani labarin na daban farfesa Ishaq Akintola, Babban Daraktan MURIC ne, ya bayyana hakan, inda ya yi nuni da kudurin dokar gyara masarautun jihar, wadda ta tsallake karatu na daya da na biyu a majalisar dokokin jihar a ranar Talata.
Idan har aka zartar da kudurin dokar za ta hana Sarkin Musulmi daga yin nadin manyan mukamai da suka hada da nada sarakuna da hakimai ba tare da amincewar gwamnati ba.
Akintola ya yi Allah-wadai da gyaran, inda ya bayyana shi a matsayin wani yunkuri na kawo cikas ga Sarkin Musulmi da kuma rage masa kima.
Ya bayar da shawarar cewa gwamnan ya shimfida harsashin ruguza Majalisar Sarkin Musulmi.
Hakan ya biyo bayan tsige sarakunan gargajiya 15 da gwamnan ya yi a baya-bayan, lamarin da Akintola ke kallonsa a matsayin wata alama ta mulkin kama-karya da kuma yunkurin mayar da lamarin siyasa.
Akintola ya bukaci ‘yan majalisar dokokin Sakkwato da su fahimci muhimmancin Majalisar Sarkin Musulmi ga sauran daukacin al’ummar Najeriya.
DUBA NAN: Sojoji Sun Kubutar Da Mata Da Kananan Yara Daga Hannun ‘Yan Ta’adda
Ya yi gargadin cewa abubuwan da ake yi a halin yanzu na iya haifar da rashin zaman lafiya da rudani ba a iya jihar ba har ma da Najeriya.