Majalisar dokokin Jihar Kano ta kuduri aniyar yi wa dokar da ta tsige Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II gyara.
Tun da farko tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ne, ya yi amfani da dokar wajen tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Sarkin Kano na 14 a 2020.
Shugaban masu rinjaye kuma wakilin mazabar Dala, Hussien Dala ne, ya gabatar da kudirin gyara dokar a yayin zaman majalisar na ranar Talata.
A shekarar 2020, kafin a tsige Sanusi II, Ganduje ya rattaba hannu kan wata doka mai cike da cece-kuce, wadda ta raba masarautar Kano zuwa masarautu biyar.
Matakin dai ya haifar da cece-kuce da rarrabuwar kawuna a tsakanin masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar.
Magoya bayan Kwankwasiyya, sun yi ta kiranye-kiranye kan a mayar da Sanusi II kan karagar mulki tare da rushe masarautun Bichi, Gaya, Rano, da kuma Karaye.
A gefe guda kuma akwai wasu ƙungiyoyi da ke adawa da rushe sabbin masarautun, inda suke kallon yunkurin a matsayin wata gaba ta yin ramuwar gayya.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran jam’iyyar NNPP, mai mulki a Jihar Kano, a baya ya taba yin tsokaci kan batun yi wa masarautun kwaskwarima bayan Abba Kabir Yusuf ya zama gwamnan jihar..
“Mun yi yakin neman zabe kuma an san mu a Nijeriya, musamman a Kano, abin da muka nuna wa jama’a shi ne da yardar Allah duk ayyukan alheri da muka fara a lokacin muna gwamnati, wannan gwamna (Abba Kabir Yusuf) da tawagarsa za su dora daga inda muka tsaya,” in ji Kwankwaso.
“A matsayinmu na dattawan wannan tafiyar, za mu ci gaba da ba su shawarar su yi abin da ya dace, mun yi kokari ba za ce komai game da batun tsige Sarki, amma yanzu dama ta samu.
“Wadanda Allah Ya yi suka zama shugabanni a yanzu, su ne ke da alhakin yanke hukunci game da masarautun, za su sake duba lamarin su yi abin da ya dace,” in ji shi.
“Baya ga batun sauya Sarki, an raba masarautar zuwa gida biyar.
Dukkaninsu za a sake duba su. Idan shugaba ya karbi mulki ko a matakin kasa, jiha ko karamar hukuma ne, yana gadar matsalolin da wasu zai iya sauya su, wasu kuma za su zama masu wahalar sauyawa.
“Muna da yakinin Allah zai bai wa gwamna (Abba Kabir Yusuf) hikimar warware matsalolin da aka kirkirar wa Jihar Kano domin kowa ya zauna lafiya a Jihar Kano,” in ji Kwankwaso.
DUBA NAN: Opay, Palmplay Da Saura Zasu Cigaba Da Karbar Sabbin Kwastomomi
Ana sa ran nan kwanaki masu zuwa majalisar dokokin Jihar Kano za ta ci gaba da yi wa dokar kwaskwarima.