Bisa dukkan alamu takaddama ta kaure tsakanin wasu gwamnonin Najeriya akan dokar hana yawon kiwo da jihohin kudancin kasar suke ci gaba da aiwatar wa wadda zata hana Fulani makiyaya zirga zirga da dabbobin su.
A karkashin dokar ana bukatar makiyaya su zauna a wuri guda domin kula da dabbobin su, sabanin yawo da shannun suna samun rikici tsakanin su da manoma, abinda ke kaiga rasa rayuka.
Dokar ta bayyana cewar duk makiyayin da aka samu yana yawo da shannun sa zai fuskanci hukunci kamar yadda dokokin kowacce jiha suka tanada.
Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu dake shugabancin gwamnonin jihohin kudu 17 yace babu gudu babu ja da baya wajen aiwatar da dokar.
Sai dai wasu gwamnonin arewacin Najeriya sun yi watsi da dokar, cikin su harda Gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufai da Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule inda suka ce tana da wahalar aiwatarwa saboda rashin yiwa makiyayan tanadi.
El Rufai wanda ya bayyana cewar dokar tana da wahalar aiwatar wa, ya kuma zargi gwamnonin kudancin Najeriyar da sanya siyasa cikin lamarin.
Gwamnan yace suma gwamnonin arewacin Najeriya sun bayyana matsayin su na kin amincewa da ci gaba da yawon kiwo, amma yace ya dace a gudanar da shirin da zai hana kiwo na dogon lokaci domin bada damar tsara yadda aikin zai yi tasiri ba tare da musgunawa makiyayan ba.
El Rufai wanda yace yana aikin samar da gandun dajin da zai ci naira biliyan 10 domin samarwa makiyayan wurin zama da kayan da suke bukata a cikin su nan da shekaru 2 masu zuwa, yace Babban Bankin Najeriya na taimakwa shirin da kudin da ya kai naira biliyan 7 da rabi.
Shima Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya bukaci Nazari akan rayuwar Fulani makiyayan da kuma samar musu mafita maimakon hana yawon kiwon kawai, inda yake cewa wannan ya sa shi rungumar shirin gwamnatin tarayya na bunkasa kiwo da ake kira ‘National Livestock Transformation Plan’.
Sule yace gwamnatin sa na shirin tsugunar da makiyayan a yankuna guda 7 dake jihar a wani hadin kai da suke da gwamnatin tarayya.