Gwamnatin Kaduna ta yi farin cikin samun labarin kisan kasurgumin dan bindigan da ya addabi Kaduna.
Dogo Maikasuwa ya shahara da hallaka mutane da yayi garkuwa da su idan aka bata masa lokaci.
Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da yan bindiga masu garkuwa da mutane suka addaba.
Jami’an tsaron Najeriya sun samu nasarar kawo karshen rayuwar shahrarren dan bindiga, ‘Dogo Maikasuwa’ wanda ya addabi al’ummar jihar Kaduna.
Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Juma’a kuma Legit Hausa ta samu.
A cewar sa, Dogo Maikasuwa, wanda aka fi sani da ‘Dogo Maimillion’ ya addabi babban titin Kaduna zuwa Kachia da kuma al’ummar Chikun-Kajuru.
Yace: “Yana daya daga cikin yan bindigan da suka fi hadari kuma suka addabi al’ummar yankin.”
“Ya shahara da mugunta kuma ya kasance mai kashe wadanda ya sace idan akayi jinkirin biyan kudin fansa ko kuma aka biya kudin da bai gamsu da su ba.”
“A ranar da dubunsa ta kare, ya shiga tarkon dakaru tare da yaransa a Gengere-Kaso a iyakan Chikun da Kajuru.”
Aruwan ya kara da cewa jami’an tsaron sun samu nasarar hallakashi tare da bindigarsa, babura biyu da rigar Soji.
Ya ce sauran yaransa sun samu nasarar tsira da raunukan amma daya daga cikinsu ya mutu kuma sun tafi da gawarsa.
Source:LEGITHAUSA