’Yan ta’adda karkashin jagorancin Dogo Giɗe sun dauki alhakin harbo jirgin yakin Rundunar Sojin Saman Nijeriya da ya fado a Jihar Neja.
A ranar Litinin rundunar ta tabbatar cewa jirginta mai saukar ungulu da ke aikin kwashe mutanen da ’yan bindiga suka addaba, ya yi hatsari, kuma ta fara bincike domin gano abin da ya faru.
Jim kadan bayan nan ne ’yan ta’adda suka fitar da wani bidiyo wanda a ciki suke ikirarin harbo jirgin sojin a yankin Badna, Gundumar Chukuba da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Ano cewa bidiyon da suka fitar ba na bogi ba ne; don haka bisa dukkan alamu sahihi ne.
Sai dai duk da haka ba za mu iya tattabar da gaskiyar ikirarin ’yan bindigar na harbo jirin sojin ta hanyar amfani da bindiga kirar AK-47 ba.
Dogo Gide na daga cikin jagororin ’yan bindigar da shi da yaransa suka addabi mazaun yankunan Jihar Neja, suna kashe manoma da jami’an tsaro.
Ko a ranar Litinin ’yan ta’adda sun kashe kimanin sojoji 20 a kan hanyar Zungeru zuwa Tegina da ke jihar a ranar Lahadi.
Majiyoyi sun tabbatar a ranar Litinin cewa ’yan bindiga 53 sun sheka lahira a yayin musayar wutar da suka yi da sojojin.
Source: LeadershipHausa