Daga karshe, direbobin manyan motocci da suka rufe babban hanyar zuwa Kaduna zuwa Kano sun bude hanyar.
Hakan na zuwa ne kimanin kwanaki biyu bayan rufe hanyar sakamakon bindige wani direba da ake zargin soja ya yi.
Mukadashin kwamandan hukumar FRSC na Kaduna ya tabbatar da bude hanyar, yana mai cewa an tattauna tsakanin direbobin da jami’an tsaro.
Awa 48 bayan da direbobin tanka suka rufe babban titin Zaria zuwa Kaduna kan zargin halaka abokin aikinsu da aka ce soja ya yi, sun yarda sun bude hanyar a ranar Asabar.
Daily Trust ta tattaro cewa direbobin tankan da suka yi amfani da motoccinsu suka rufe hanyar sun yarda za su janye motoccin bayan tattaunawa da aka yi da su da jami’an tsaro da FRSC.
Direbobin Manyan Motocci Da Suke Katse Hanyar Kaduna Zuwa Kano Sun Janye Motoccinsu Bayan Awa 48.
A ranar Laraba ne aka rahoto cewa wani soja da ke aiki da kamfanin gini ya bindige wani direba bayan rikici ya shiga tsakaninsu.
Direbobin sun rufe hanyar sun nemi a yi wa abokin aikinsu da aka kashe adalci da iyalansa.
Lamarin ya faru ne kusa da Tashar Yari da ke garin Makarfi kan babban hanyar, hakan ya janyo cikinson ababen hawa.
Da ya ke tabbatar da bude hanyar a safiyar ranar Asabar, mukadashin kwamandan FRSC na jihar, Lawal Garba, ya ce al’amura sun koma yadda suke.
Ya ce: “Ina farin cikin sanar da kai cewa a safiyar yau an bude babban hanyar Zaria zuwa Kano misalin karfe 9.30 na safe kwanaki bayan rufe shi.
Babu cinkoso yanzu. Jami’an mu na kula da hanyar.”
Rundunar yan sandan jihar ta bada umurnin yin cikakken bindike kan kashe direban da sojan ya yi.
Jami’an tsaro sun kwato motoccin da aka sace daga Najeriya aka tafi da su Jamhuriyar Nijar.
A wani rahoton, yan sanda na Najeriya tare da hadin gwiwar yan sandan kasa da kasa ta Interpol sun kwato wasu motocci da aka sace daga Najeriya aka tafi da su Nijar.
Kakakin yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ne ya sanar da hakan kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto.
Adejobi ya ce babban sufetan yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya jinjinawa hadin gwiwar da aka yi tsakanin kasashen duniya 194 don kama masu laifi.