Wasu yan bindiga sun halaka wasu mutane hudu a yankin Sapele da ke jihar Delta a ranar Laraba.
Daga cikin wadanda aka kashe harda wani kansila a yankin Warri ta arewa, Bigha Grikpa Da yake tabbatar da lamarin, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Edafe Bright (DSP), ya ce mutum biyu aka kashe.
Wasu tsagerun yan bindiga sun kaddamar da sabon a garin Sapele da ke jihar Delta inda suka kashe wani mataimakin shugaban yankin Warri ta arewa, Bigha Grikpa, da wasu uku a ranar Laraba.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa yan bindiga da suka kai mamaya yankin da sanyin safiya ne suka bindige Gikpa har lahira.
Wata majiya ta ce dan siyasan da sauran mutanen da abun ya ritsa da su sun isa wajen da bai dace ba a daidai lokacin da bai kamata ba.
Kisan na zuwa ne a daidai lokacin da aka gano gawawwakin wasu matasa biyu da aka kaddamar da nemansu bayan sun bata kwanaki biyu da suka gabata.
Rundunar yan sanda ta yi martani
Da aka tuntube shi don jin ta bakinsa kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, Edafe Bright (DSP), ya ce mutum biyu aka kashe a karon na yan kungiyar asiri, jaridar Vanguard ta rahoto.
Wasu majiyoyi da dama sun tabbatar da lamarin sannann an tattaro cewa garin na ta zuban jini tun tsawon shekaru biyu da suka gabata yayin da ake kashe matasa a lokacin kirsimeti.
Mutanen da aka kashe a ranar Laraba sun hada da Mathew Ekiopa, wanda ke da shagon siyar da kayan kanti a Lexi Junction, da budurwar da ke masa jiran shagonsa mai suna Blessing.
An kuma tattaro cewa an harbe su ne a kai da kafada a nan gaban shagon.
Mutum na hudu da aka kashe sunansa Alhaji Bello, wani dan kasuwa wanda ke siyayya a shagon lokacin da yan bindigar suka kai farmaki.
Wani mazaunin yankin mai suna Khalil Samuel, ya koka kan yawan kashe-kashe da ake fama da shi a yankin a shafinsa na Facebook yana mai cewa: “An kashe mutane hudu a Sapele a safiyar nan (Laraba). Sapele na matukar bukatar taimako.”
Khalil ya bukaci gwamnati da ta sanya dokar kulle a garin yana mai cewa kashe-kashen ba abun da za a lamunta bane.
Wani tsohon dan majalisar jihar, Daniel Mayuku, ya nuna kaduwa kan mutuwar Grikpa.
Ya ce: “Na san wannan kansilan mai saukin kai da mutunta mutum. Menene laifinsa?”
A wani labari na daban, mun ji cewa an murkushe wasu yan bindiga da masu garkuwa da mutane a wata musayar wuta da suka yi da jami’an tsaro a karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.