Deji Adeyanju, dan gwagwarmaya kuma shugaban kungiyar ‘Concerned Nigerians’ ya gargadi tsohon Shugaban kasa Jonathan ya yi hankali da APC da Tinubu.
Adeyanju ya yi wannan gargadin ne a rubutun da ya wallafa a shafinsa na Facebook yana mai cewa ‘za a yi amfani da tsohon shugaban kasar ne kuma a yi watsi da shi’.
Dan gwagwarmyar ya yi wannan tsokacin ne a matsayin martani kan ziyarar da Tinubu da Kashim Shettima da gwamnonin APC suka kai wa Jonathan a gidan sa.
Dan gwagwarmaya kuma shugaban ‘Concerned Nigerians’, Deji Adeyanju ya ce APC tana shirin amfani da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne sannan ta yi watsi da shi.
Ya yi wannan tsokacin ne bayan ziyarar baya-bayan nan da dan takarar na APC, Asiwaju Bola Tinubu ya kai wa Jonathan a daren ranar Talata a Abuja.
Adeyanju ya tunawa tsohon shugaban kasar rawar da yan APC suka taka yayin zaben fidda gwaninsu na shugaban kasa, yana cewa tun farko ya masa gargadin ‘za su yi amfani da shi su watsar.’
Adeyanju ya ce: “Goodluck Jonathan, ba za ka mutu ba idan ba ka mara wa kowa baya ba a wannan zaben.
Yayin zaben fidda gwanin APC lokacin da kabal ke rudarka, da fatan ka tuna dukkan gargadin da na maka cewa za su yi amfani da kai ne su watsar.”
Legit Hausa ra rahoto cewa wadanda suka yi wa Tinubu rakiya yayin ziyarar sun hada da abokin takararsa, Kashim Shettima, da gwamnonin APC biyar da suka hada da Simon Lalong na Plateau, Muhammadu Badaru na Jigawa, Bello Matawalle na Zamfara, AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara da Dapo Abiodun na Ogun.
Jam’iyya Tayi Karin Haske Duk da cewa ba a bayyana dalilin ziyarar ba, wata majiya daga bangaren Tinubu ta ce ziyarar na tuntuba ne gabanin babban zaben shugaban kasa na 2023, The Punch ta rahoto.
Majiyar ta ce: “Bai kamata ziyarar da ya kai wa Jonathan ya bada mamaki ba. Tinubu baya gaba da dukkanin shugabannin siyasa na jam’iyyarsa ko na adawa.”
Source: LEGITHAUSA