Dattawan arewa sun shawarci yan Najeriya da su bincika tare da latsa dukkan masu son darewa kujerar shugaban kasa a 2023.
Mai magana da yawun NEF, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce akwai bukatar al’ummar kasar su tambayi yan takarar kan yadda za su magance matsalolin kasar idan aka zabe su.
Sun kuma yi kira ga takwarorinsu na sauran yankunan kasar a kan su kwaikwayi abun da suka yi na kiran yan takarar don su baje masu kolin monufofin su.
Kungiyar dattawan arewa ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su tambayi yan takarar shugaban kasa kan yadda zasu magance matsalolin kasar idan aka zabe su.
Kakakin kungiyar NEF, Hakeem Baba-Ahmed ne ya bayyana haka yayin da ya fito a shirin Sunday Politics na Channels TV.
Ya ce: “Akwai bukatar yan Najeriya su latsa yan takararmu. Ya kamata mu gano wa za mu yarda da shi a cikin wadannan mutane.”
Yayin da manyan yan takara da suka hada da Peter Obi na LP, Atiku Abubakar na PDP, Bola Tinubu na APC da Rabiu Kwankwaso na NNPP ke da tarin kwarewa, ya ce ya kamata su nunawa ‘yan Najeriya hanyar da za su bi don shawo kan manyan matsalolin kasar, rahoton Daily Post.
Baba-Ahmed ya kara da cewa: “Wadannan mutane ne masu tarin kwarewa a fannin shugabantar mutane.
Wadannan mutane ne masu nauyin aljihu tunda har suka kai matakin da suke yanzu na yan takara.
Yakamata a binciki halayyarsu.
” Ya ce taron da kungiyar ta kira kwanaki don ba yan takarar damar fadawa yankin arewa da yan Najeriya tanadin da suka yi masu ne idan aka zabe su a 2023.
A cewarsa, ya kamata sauran yankuna su yi koyi da irin wannan tattaunawar don yan Najeriya su samu damar yin zabi nagari a shekara mai zuwa.”
“Idan za a iya maimaita shi a sauran hanyoyi, ya kamata ayi hakan. Akwai bukatar a latsa wadannan yan takara kai tsaya su fadi abun da suke son yi.”
Ya ce kungiyar dattawan za ta yi nazari kan manufofin yan takarar domin ba ‘ya’yanta karin haske kan abun da za su iya yi.
Shettima Ya Magantu Kan Tattaunawa da Kwankwaso.
Ya Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023
A wani labarin, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya magantu a kan yiwuwar hadakarsu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso gabannin zaben 2023.
Daily Trust ta rahoto cewa Shettima ya bayyana cewa shi da kansa zai nemi Kwankwaso a daidai lokacin da ya kamata.
Tsohon gwamnan na jihar Borno wanda ke gabatar da jawabi a taron kungiyar limaman birnin tarayya Abuja, yana barkwanci ne da tsohon dan majalisar wakilai, Garba Ibrahim Muhammed, wanda ya wakilci Sanata Kwankwaso a taron.
Source;legithausang