Manyan kamfanoni da attajirai a Najeriya irin su Dantata sun tattara kudade domin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a Jigawa.
Dantata da Abdulsamad na daga cikin wadanda suka ba da tallafin a wani taron da aka gudanar a jihar.
A daminan bana ne aka samu mummunar ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyyar rasa dukiyoyi da rayukan jama’a a jihar Jigawa da bangarori da yawa na kasar nan.
‘Yan kasuwan Najeriya, Aminu Dantata da mai kamfanin BUA Group, Abdulsamad Rabiu da sauran masu tallafawa jama’a sun tattara N1bn domin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa dasu a jihar Jigawa.
An bayyana ba da wannan tallafi ne a birnin Dutse a jihar a wani taron tattara kudin tallafi na 2022 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar, Leadership ta ruwaito.
Kowanne daga ‘yan kasuwan ya ba da tallafin N200m, gwamnatin Jigawa ta ba da N250m yayin da gwamna Badaru da kansa ya ba da N25m a madadin iyalansa da kamfamin Talamis Group.
Dantata, wanda ya samu wakilcin Salisu Sambajo ya bayyana damuwa game da halin da jama’a suka shiga sakamakon wannan ambaliya.
A bangare guda, wadanda suka ba da tallafin sun yi addu’ar neman gafara ga wadanda suka mutu a wannan lamari tare da jajantawa wadanda suka rasa kadarori da amfanin gonakinsu.
Gwamna Badaru ya yabawa wadanda suka ba da tallafin, ya kuma bukaci kwamitin rarraba tallafin da su yi gaskiya wurin rarraba kudaden da aka ba jama’a a jihar.
Shugaban kwamitin, Bashir Dalhatu (Wazirin Dutse), kuma tsohon ministan makamashi ya godewa su Dantata da kamfanonin da suka ba da tallafin, Premium Times ta ruwaito.
Sauran wadanda suka ba da tallafin sun hada da mambobin majalisar dokokin a matakin jiha da tarayya da kuma shuganannin kananan hukumomi.
Hakazalika, bankin Zenith, Jaiz, FCMB, Sterling, Guaranty Trust da Unity na daga cikin kamfanonin da suka ba da tallafi.
Adadin wadanda suka shiga tasku dalilin ambaliyar ruwa A wani labarin kuwa, wnai rahoto ya bayyana adadin wadanda suka mutu a sanadiyyar ambaliyar ruwan da aka yi a jihar ta Jigawa.
A cewar rahoton, akalla mutane 60 suka rasa rayukansu sakamakon mamakon ruwa da aka yi a jihar a daminan bana.
Tuni dai hukumomin agaji da kula da ‘yan gudun hijira suka fara kokarin shawo kan lamari da kuma taimakawa wadanda abin ya faru dasu.
Source:Legithausa