Attajirin nan na yankin Afrika Alhaji Aliko Dangote gaba daya yayi babban alkawari ga daliban jami’ar KUST dake Kano.
An mayar da sunan jami’ar ta KUST sunan Alhaji Aliko Dangote kuma kai tsaye an fara ganin aiki.
Attajirin haka kuma ya dauki sabbin Farfesoshi goma sha biyar daga kasashen waje don karawa jami’ar kwarjini.
Shugaban kamfanonin Dangote, ya yi alkawarin bada gurbin aiki ga duk dalibin jami’ar kimiya da fasahan jihar Kano Wudil da ya kammala karatu da 1st Class ko Second Class Upper.
Shugaban jami’ar, Farfesa Shehu Musa, ya sanar da hakan ga manema labarai ranar Juma’a a Kano yayin sanar da mayar da sunan jami’ar ‘Aliko Dangote University’, rahoton DailyTrust.
Musa ya kara da cewa ya yi alkawarin dauko Farfesoshi guda 15 daga kasashen waje tare da gina musu gidaje da biyan albashinsu.
Yace an tuni an fara shirin daukan Farfesoshin kuma sa hannun Dangote kawai ake jira.
Ya yi kira ga manyan attajirai su kwaikwayi hali irinta Attajirin wajen zuba jar harkar Ilimi don amfanin kasar.
Ya mika godiyarsa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da mambobin majalisar dokokin jihar bisa sauyin sunan da suka yiwa jami’ar.
Jamia’ar wacce ke garin wudil tana koyar da fannonin kimiyyar kere kere.
Source:legithausang