Janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya ya gabatar da jawabi a kan batun tsaro da shirin zabe.
Tsohon Ministan harkokin cikin gidan yana zargin ‘yan siyasa da laifin matsalolin da ake samu.
Da yake jawabi a taron, an fahimci Dambazau yana ganin jami’an tsaro sun yi wa zaben 2023 tanadi.
Janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya ya zargi ‘yan siyasa da hannu a matsalolin rashin tsaro da ake fama da shi a bangarorin kasar nan.
Abdulrahman Dambazau ya halarci wani taro da kungiyar I Am Change ta shirya a garin Abuja.
The Cable ta ce ya gabatar da jawabi kan inda ya kware.
Taron da aka yi ranar Alhamis a dakin taro na ‘Yaradua ya tabo lamarin barazanar tsaro yayin da ake shirin gudanar da babban zabe nan da ‘yan kwanaki.
Tsohon shugaban hafsun sojan kasar ya shaida cewa jami’an tsaro sun yi bakin kokarinsu a wajen magance matsalolin rashin tsaro a zabe mai zuwa.
Babu zabe inda babu jami’an tsaro Janar Abdulrahman Dambazau (rtd) yake cewa sai da jami’an tsaro za a iya shirya zabe na kwarai.
An rahoto tsohon Ministan harkokin cikin gidan yana cewa an kawo rashin zaman lafiya a dalilin irin kazamar siyasar da aka bijiro da ita a halin yanzu.
Maganar Janar Abdulrahman Dambazau (rtd) “Mai girma shugaban kasa ya fada sau da-dama cewa yana so a yi zaben adalci na gaskiya, kuma ba za mu iya zaben kwarai ba tare da cikakken tsaro ba.
Shekarun baya, hankalinmu yana kan Arewa maso gabas, yanzu mun koma kan Kudu maso gabas da inda da ake garkuwa da mutane da rikicin makiyaya.
Musamman a Kudu maso gabas, inda haramtaciyyar kungiyar IPOB ta rantse ba za ayi zabe ba.
Saboda haka, irin kalubalen da nake magana kenan, kuma na tabbata cewa hukumomin tsaro sun yi bakin kokarinsu wajen ganin sun magance lamarin. – Abdulrahman Dambazau
Inda ‘yan siyasa suka shigo ‘Yan siyasa da kansu suka kirkiri wasu daga cikin kalubalen tsaron nan saboda ana siyasar kabilanci, siyasar addini, da kuma siyasar bangaranci.
Wadannan ke raba kan jama’a, su jawo tashin-tashina. Ina ganin ya kamata ‘yan siyasa su nuna kishin kasa, su yi abin da ya fi dacewa da kasar nan.” – Abdulrahman Dambazau
Source: LegitHausa