Jami’an hukumar kwastam sun bayyana dalilin kwace wasu kaya da suka yi wadanda aka shigo dasu daga kasar Chana a kan titin Lokoja zuwa Abaji.
Hukumar ta bayyana cewa, kayan an yi rubutu a kansu da yaren Chana wanda idan za a shigo da kaya Najeriya, da Turanci ake yin bayanin su.
Kayayyakin sun hada da kwali 4,289 na lemukan Chana, galan 204 na miya, taliya, garin tuwo, fulawa sauransu yayin da aka kwace tayoyi 2,300 a titin Mokwa.
Tawaga ta musamman ta shugaban hukumar kwastam ta kasa ta sanar da dalilin ta kwace wasu kayan da aka shigo dasu daga Chana da wasu kayan sumogal ta babban titin Lokoja zuwa Abaji, jaridar Daily Trust ta rahoto.
A yayin jawabi ga manema labarai kan wannan cigaban, Kodinetan tawagar na hedkwatar, mataimakin shugaba Kolapo Oladeji yace kayayyakin da aka kwace an shigo dasu ne ba bisa ka’ida ba kuma sun take dokoki da ka’idoji.
Kamar yadda yace: “Daya daga cikin dokokin shigo da kaya Najeriya shi ne dole a yi rubutun su da turanci, amma kayan da aka kwace an yi rubutunsu ne da yaren Chana kuma ya ci karo da dokokin shigo da kaya na sashi na 146 sakin layi na E na SEMA 2004 CAP 45 na dokokin Najeriya.”
“An kama kayan ne a kan babbar hanyar Abaji zuwa Lokoja kuma sun hada da kwali 4,289 na lemukan Chana, galan 204 na miya, taliya, samanbita, fulawa da sauransu.” – Yace.
An kama tayoyi 2,300 Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, DC Oladeji ya kara da cewa, tawagar ta kwace tayoyi 2,300 kan babban titin Mokwa dake jihar Niger.
Yace binciken farko yanzu aka fara kan yadda kayan suka shigo Najeriya kuma har suka bar iyakoki inda ya kara da cewa za a dauka mataki bayan gama bincike.
Ya kara da cewa, tawagar ta fara aiki da fasahar zamani domin inganta binciken sirri yayin da take kira ga duk masu shigo da kaya ta halastacciyar hanya da su tabbatar da cewa sun bi dokokin da suka dace yayin kasuwancinsu.
Jami’an Kwastam sun kwace kaya a Katsina
A wani labari na daban, Hukumar kwastam ta kasa reshen jihar Katsina ta sanar da kama kayan miliyan 79 a jihar Katsina a cikin wata biyu.
Kayayyakin da ta kama sun hada da motar hawa, jarkokin mai, buhunan shinkafa da sauran su.