A farkon makon nan ne aka samu barazanar kai harin ‘yan bindiga a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Sakkwato, inda aka rika aika sakonnin waya ga iyayen yara cewa kowa ya zo ya dauki yaronsa an rufe makarantar.
Sai dai kuma, kwana daya da yin hakan, wata majiya ta bayyana mana cewa asalin barazanar da aka samu ba daga ‘yan bindiga ba ne, daga wani dalibi ne da yake tsananin son zuwa gida.
“Ana cikin haka ne sai aka wayi gari daya daga cikin daliban da suka matsu su koma gida, kawai ya yanke shawarar rubuta wasika ya mammanna a wasu muhimman wurare da ke makarantar, wadda shi a tunaninsa, hakan zai tilasta wa mahukuntan makarantar su rufe makarantar, abin da ya aikata ya rikita daukacin makarantar, malamai da dalibai suka shiga dimuwa kowa yana neman inda zai sa kansa. Wasu daga cikin daliban ma suka nuna zakuwa sosai a kan a bar su, su koma gida.”
Majiyar ta mu ta kuma bayyana yadda hankula suka kwanta bayan an gano dalibin da ya yi wannan danyen aiki.
“Yanzu haka, komai ya yi daidai, an kawo karshen wannan rudani, hukumar makaranta ta gano dalibin da ya shirya wannan abu domin ya kawo rudani, an riga an sanar da iyayensa, an sanar da jami’an tsaro kuma tuni suka dauki mataki na dawo da doka a makarantar. Sai dai kuma daga bisani bayan hukumar makarantar ta tuntubi ma’aikatar ilimi ta tarayya, ta rufe makarantar. Kodayake dama wasu dalibai sun riga sun kammala jarrabawarsu ta karshen zango za su fara hutu daga ranar 16 ga Satumbar 2021, ka ga ana sauran kwana biyu ma kenan su fara hutun sai aka rufe”. In ji majiyar tamu.