Hukumomi a kasar Burtaniya sun dura gidan wani dalibi dan Najeriya, inda suka gano tsabar kudi da suka kai $8.5m.
Kudaden da aka gani cikin nau’ikan daloli daban-daban an ajiye su ne a cikin wani akwati, kamar yadda yake a wani bidiyo.
Mutumin da aka kaman yana magana da daya daga cikin harsunan Najeriya, ya kuma bayyana cewa shi dalibi ne a kasar.
Wani bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna lokacin da hukumomin kasar Burtaniya suka shiga gidan wani dalibi dan Najeriya, suka bankado wasu kudade masu yawa.
An ruwaito cewa, an kama wannan dalibi ne da wasu daloli a cikin akwati, yawansu ya kai akalla $8.5m.
Bidiyon, wanda wani yanki ne na ayyukan kakkabe ta’addanci a Burtaniya, ya nuna dalla-dalla yadda aka dura gidan dalibin dan Najeriya da kuma yadda aka gano kudaden da ya boye.
Hukumomin sun shiga gidan dalibi din ne, da nufin bincike, sai kawai suka gano kudade a daure cikin wani akwati da aka boye.
Kada ka bari komai ya wuce ka Watakila kudaden harkallar haramun ne.
A cewar bidiyon, akwai yiwuwar kudaden da aka gano na aikin ta’addanci ne, damfara ko kuma mallaki ne da wani dan Najeriya mai tafiyar da harkallar miyagun kwayoyi a Burtaniya.
Jim kadan aka ga wani matashi dan Najeriya ya shigo, inda ya nemi a bashi damar daukar littafinsa amma aka hana shi.
Daga nan dalibin ya fara kiran waya yana magana da harshen Yarbanci.
Shin kudaden nan da ‘yan siyasa ne?
Ba a dai bayyana ko kudin mallakin daliban bane, ko kuma shi ake zargi da adana kudi masu yawan da suka wuce misali.
Wasu ‘yan Najeriya na kan ra’ayin cewa, watakila da ne ga wani fitaccen dan siyasan Najeriya da ya saci kudi ya tsallaka dasu kasar waje.
Ya zuwa yanzu dai, kama ‘yan Najeriya da kudaden da ake zargin na sata ne ko na wata harkallar da bata dace ba.
Bayyana sauya fasalin kudi a Najeriya na ci gaba da jawo cece-kuce a kasar, kuma hakan ya kai ga bankado kudade da yawa.
Babban bankin Najeriya ya yi karin haske kan nau’in kudaden da za a sauya da kuma yiwuwar kirkirar sabon nau’in kudi.
Hakazalika, ya yi bayani kan cece-kuce da ake yadawa kan cire rubutun Ajami a jikin kudin Najeriya.
Source:LEGITHAUSA