Wata dalibar Kwalejin ilimi ta gwamnatin Tarayya dake Zariya, wato FCE Zariya ta bace bat a yau Asabar 10 ga watan Yulin 2021 bayan da ta fita daga gidansu dake Kaura cikin birnin Zariya zuwa makarantar FCE dake Unguwar Gyallesu duk a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.
Lamarin ya auku ne da safiyar yau Asabar, inda da misalin karfe 9 da mintoci na safe ta aikawa mahaifiyarta sako cewa; “Mama ina neman addu’arku, na fada hannunsu”.
Mahaifinta ya shaidawa wakilin Nigeria21 Hausa cewa; “bayan ta aikawa mahaifiyarta sakon nan, an kira lambarta ba ya zuwa har ya zuwa yanzu”, kamar yadda ya tabbatar mana.
Dalibar mai suna Rahmatu A. Sambo tana karatun ‘part-time’ ne a bangaren lissafi da ilimin sinadarai (Maths/Chemistry).
Wadansu bayanai sun nuna cewa dalibar ta saba hawa babur ne a duk lokacin da za ta tafi makaranta daga gida.
Ya zuwa hada rahoton nan babu cikakken bayanin kan inda dalibar take, sai dai al’umma na ta tururuwa zuwa gidan iyayen dalibar domin taya su alhini da addu’ar Allah ya bayyanata.