A jiya Juma’a ne daliban Nijeriya suka bi sahun tsari da kudurorin gwamnati mai jiran gado take fatan zuwa da shi, inda suka bukaci zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya tabbatar da ingantaccen tsaro da samar da ingantaccen ilimi a gwamnatinsa.
Har ila yau, a cikin jerin bukatun da suka gabatar a gaban gwamnati mai zuwa akwai samar da tsayayyiyar wutar lantarki da kuma dabarun yaki da dakile yunwa da fatara da daukaka darajar Nijeriya ta hanyar amfani da kyawawan manufofi.
Galibin yaran Nijeriya, wasu na ta gararanba a kan tituna, suna fuskantar matsalolin damuwa da shaye-shayen miyagun kwayoyi, safarar mutane, fyade, tashin hankali talauci da dai sauransu.
Wani bangare na daliban da suka zanta da manema labarai a fadin kasar, sun yi kira ga Tinubu da ya magance matsalar rashin tsaro, musamman a makarantu da samar da yanayin da daliban da suka rasa matsugunansu za su koma makaranta.
Yaran ‘yan makarantar sun koka da cewa a halin yanzu yawancinsu suna karatu a cikin yanayi na tsoro da rashin tabbas, wanda hakan ke jawo musu rugujewar tunani saboda tsoron abin da ba a sani ba.
Daliban da suka yi magana game da abin da suke sa rai daga gwamnati mai zuwa a wani bangare na ayyukan tunawa da ranar yara ta bana, sun kuma bukaci Tinubu da ya gaggauta sake fasalin Nijeriya musanman yaki da yunwa.
Daliban sun kuma roki gwamnatin tarayya da ta ci gaba da gudanar da shirin ciyar da makarantu na kasa domin bunkasa ilimin boko da bunkasa noma.
A wata tattaunawa da suka yi da LEADERSHIP, daliban sun bukaci gwamnati mai jiran gado da ta magance matsalolin da ke hana yara zuwa makaranta, wanda ya haifar da yara sama da miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta.
A Abuja, wasu yaran ‘yan makaranta da suka zanta da wakilinmu sun roki gwamnatin da ta magance matsalar sace yara ‘yan makaranta da ta addabe su, tare da ba su kariya a matsayinsu na shugabannin Nijeriya a gobe.
Wata dalibar Sakandaren Gwamnati Garki da ke Abuja, Emmanuel Pamela, ta ce kalubalen farko da za ta so gwamnati ta tunkara shi ne rashin tsaro.
Pamela ta ce, “Na tabbata kowa na son Nijeriya da inda yake aiki, zai ji dadi matsawar aka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
“Ina son gwamnati mai zuwa ta tabbatar da cewa dukkan yara suna makaranta tare da tabbatar da tsaro ga yaran.”